Aliyu Cisse
From Wikipedia, the free encyclopedia
Aliou Cissé (an haife shi A ranar 24 ga watan Maris shekarar 1976) kocin ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Senegal kuma tsohon ɗan wasa wanda shine manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal . Cissé sananne ne da kyaftin din tawagar Senegal da ta kai wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a shekarar 2002 da kuma kasancewa kocin Senegal na farko da ya lashe gasar a shekarar 2022 bayan ya kai wasan karshe a shekarar 2019 .
Aliyu Cisse | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Ziguinchor (en) , 24 ga Maris, 1976 (47 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Senegal Faransa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football national coach (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 180 cm |
Bayan ya fara aikinsa a Faransa, daga baya ya taka leda a kungiyoyin Ingila Birmingham City da Portsmouth . Cissé ya kasance dan wasan tsakiya na tsaro wanda kuma, a wani lokaci, ya taka leda a tsakiya.
Cissé ya kasance babban kocin Senegal tun a shekarar 2015, bayan da ya karbi ragamar horas da su na dan lokaci bayan korar Amara Traoré, a matsayin riko a shekarar 2012. Ya kuma kasance mataimakin kocin kungiyar 'yan kasa da shekaru 23 daga 2012 zuwa shekarar 2013, inda ya zama babban koci daga 2013 zuwa 2015.