Haƙƙoƙi
Haƙƙin da halittu ke dasu na ɗabi'a ko akan ƙudurin doka, zamantakewa, ko sanannun ɗabi'o'in yanci ko mallaka akan wasu tsarin doka, yarjejeniyar al'umma ko kuma ɗabi'a tabbatattu. / From Wikipedia, the free encyclopedia
Haƙƙoƙi kamar yadda akafi sani shine Haƙƙi wasu dokoki ne, na zamantakewa ko kuma ƙa'idojin dabi'u na 'yanci ko kuma na mallaka; wato haƙƙoƙi wasu dokokin rayuwa ne na yau da kullum akan abubuwan da aka yarjewa mutane ko halayen da kuma ake tsammani daga garesu dangane da tsarin shari'a, tsarin zamantakewa, ko kuma hukunce-hukuncen dabi'a.[1] Haƙƙoƙi na da muhimmanci ga nazarin dokoki ko kuma dabi'u
Haƙƙoƙi | |
---|---|
legal relationship (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | legal concept (en) da yarjejeniya |
Bisa | right-to-left (en) |
Karatun ta | jurisprudence (en) |
Hannun riga da | duty (en) |
Equivalent property (en) | http://purl.org/dc/terms/rights |
Ana ɗaukar ƴanci da zama mafarin wayewar kai (civilization) ga duk al'umman da suka cigaba, saboda ana ɗaukarsu a zaman ginshiƙan zaman al'umma da al'adu. [2] Tarihin rikice-rikicen zamantakewa na da alaka da yunkurin bayyan hokkoki da kuma jaddada su. A cewar Stanford Encyclopedia ta Falsafa, "tsarin mallakar hakƙoƙi shine mafarin tsarin gwamnatoci, da abubuwan da suka ƙunshi dokoki, da kuma zama magyarin tsarin kyawawan ɗabi'u kamar yadda ake gani a halin yanzu".[1]