Idriss Déby
From Wikipedia, the free encyclopedia
Marshal Idriss Deby Derby (Larabci: إدريس ديبي Idrīs Daybī Itnū; an haife shi a ranar 18 ga watan Yunin, 1952 -ya mutu a ranar 20 ga Afrilun 2021) ɗan siyasan Chadi ne kuma hafsan soja wanda ya kasance Shugaban kasar Chadi daga shekara ta 1990 har zuwa karshen rayuwarsa a shekara ta 2021. Ya kuma kasance shugaban Jam’iyyar Ceto Patriotic Salvation Movement. Déby dan asalin Bidyat ne na ƙabilar Zaghawa. Ya karɓi mulki ta hanyar jagorantar tawaye ga Shugaba Hissène Habré a cikin watan Disamban shekara ta 1990 kuma ya tsira daga tawaye daban-daban da yunƙurin juyin mulki ga mulkin nasa.idriss Déby ya ci zabe a shekara ta 1996 da shekara ta 2001, kuma bayan an daina kayyade wa'adi sai ya sake cin nasara a shekara ta 2006, 2011, 2016, da kuma shekara ta 2021. Ya kara da "Itno" a cikin sunan mahaifinsa a cikin watan Janairu shekara ta 2006. Ya kammala karatun digiri na Cibiyar Juyin Juya Hali ta Muammar Gaddafi. Yawancin kafofin yada labarai na duniya sun bayyana mulkin idriss Déby na shekaru goma a matsayin mai iko. An kashe shi a cikin watan Afrilu shekara ta 2021 yayin da yake ba da umarni ga sojojinsa kan 'yan tawaye daga kungiyar Front for Change da Concord a Chadi (FACT).
Idriss Déby | |||||
---|---|---|---|---|---|
30 ga Janairu, 2016 - 30 ga Janairu, 2017 ← Robert Mugabe - Alpha Condé (en) →
2 Disamba 1990 - 20 ga Afirilu, 2021 ← Hissène Habré - Mahamat Déby Itno → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Fada (en) , 18 ga Yuni, 1952 | ||||
ƙasa | Cadi | ||||
Ƙabila | Zaghawa people (en) | ||||
Harshen uwa |
Larabci Zaghawa | ||||
Mutuwa | Ndjamena, 20 ga Afirilu, 2021 | ||||
Makwanci | Amdjarass (en) | ||||
Yanayin mutuwa | death in battle (en) (gunshot wound (en) ) | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Hinda Déby Itno | ||||
Yara | |||||
Karatu | |||||
Makaranta | Institut aéronautique et école de pilotage Amaury de la Grange (en) | ||||
Harsuna |
Faransanci Larabci Zaghawa | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||
Kyaututtuka | |||||
Aikin soja | |||||
Fannin soja | Chadian ground forces (en) | ||||
Digiri | field marshal (en) | ||||
Ya faɗaci |
Battle of N'Djamena (en) Yaƙin Basasar Chadi (2005–2010) Northern Chad offensive (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | Patriotic Salvation Movement (en) | ||||