Iraki (ko Iraƙ) kasa ce ta larabawa da ke a nahiyar Yammacin Asiya. Iraki ta hada iyaka da kasar Turkiya daga arewa, kasar Iran daga gabas, Persian Gulf da kasar Kuwaiti daga kudu maso gabas, kasar Saudiyya daga kudu, kasar Jodan daga kudu maso yamma, sai kuma kasar Siriya daga yamma. Babban birnin Iraki itace Bagdaza kuma itace birni mafi girma a kasar. Kasar Iraki gida ne ga kabilu da dama, irinsu, Mutanen Iraqi, Kurdawa, Mutanen Assyriya, Armaniyawar Iraki, Yazidi, Mandaeans, Iranians in Iraq, Shabaks da kuma sauran dumbi sauran tsaunuka da kasa da dabbobi. Mafi akasari daga mutum mliyan 44 na kasar Musulmai ne, sauran addinai kuma sun hada da Kiristanci, Yazidism, Mandaeism,Ahl-e Haqq, da kuma Zoroastra.[1][2] Harshen gwamnati na kasar Iraki itace Larabci da kuma Kurdusanci. Sauran sanannun harsuna a yankin sun hada da harsunan Neo-Aramaic, Turkanci da kuma harsunan Armeniya.[3]