Lissafi
From Wikipedia, the free encyclopedia
Lissafi ko kuma nazarin kidaya wani fanni ne na ilimi wanda yake taimakawa dan'adam yin kidaya da sanin yawan abubuwa da kuma sanin tsarin yadda abubuwa suke idan an cenza su ta wata suffar. Ko kuma Ilimi ne na fasaha wanda ake koyan yadda ake tsare tsare, zane-zane da kuma kere-kere ta hanya mai sauki.
Lissafi | |
---|---|
academic discipline (en) , academic major (en) da mathematical term (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | natural science (en) |
Bangare na | science, technology, engineering, and mathematics (en) , formal science (en) da exact science (en) |
Amfani | ilmi, mathematical modelling (en) , engineering (en) , finance (en) da computation (en) |
Suna a harshen gida | μᾰθημᾰτικά |
Is the study of (en) | mathematical object (en) |
Hashtag (en) | math, mathematics da maths |
Has characteristic (en) | mathematical beauty (en) , formalization (en) da har’abada |
Tarihin maudu'i | tarihin lissafi da bayanan lissafi |
Gudanarwan | masanin lissafi da mathematics student (en) |
WordLift URL (en) | http://data.thenextweb.com/tnw/entity/mathematics |
Stack Exchange site URL (en) | https://math.stackexchange.com |
Shi Lissafi ya rabu kashi biyu: Lissafi wani fannin ilimi ne da ya shafi nazarin 'ya'yan kididdiga adadi, sarari, tsari, yanayi da sauyi.ana amfani da ilimin lissafi a bangarori da dama kamar; kimiyya, kanikanci, likitanci da kimiyyar zaman takewa. Amfanin ilimin lissafi a wadansu lokuta shike haifar da sabbin rassa a fannin kamar lissafin kididdiga.kuma masana lissafi suna anfani da lissafi tsagwaran sa, ba don wani dalili ba, Ba wani abu dazai iya bayyana maka wannan lissafi ne na amfani ko kuma a'a.
- (1) akwai lissafi na lambobi, kasafi da kidaya wato (hadawa, rubawa, rabawa da kuma fiddawa) wadda ake kira Aljebra.
- (2) Akwai kuma lissafi na zane-zane, kirkire-kirkire da sauransu da ake kira Geometri.
Geometri tana taimakawa wajen sanin suffar abu: wato tsawonsa, fadinsa, girmansa da yawansa. Tana taimaka mana a takaice a cikin fannin gini, kira da kuma suffur
Ana yin lissafi kafin ayi wani abu domin a san me nene sakamakon abun idan ya faru wannan bangaren na lissafi ana kiransa Kasafi wato "statistics" a turance. A cikin wannan fanni na Kasafi a kan hada gamayyar abubuwa a yi nazari akan sakamakon da za su bayar idan anyi wani abu akan su ta hanyar anfani da alkalamomin da su ke a cikin su.