Luis Muriel
From Wikipedia, the free encyclopedia
Luis Fernando Muriel Fruto (an haife shi 16 Afrilu a shekarai 1991) ƙwararren ɗan wasan gaba nedan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Colombia wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba a ƙungiyar Atalanta dake qasar italiya Serie A da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Colombia .
Luis Muriel | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Luis Fernando Muriel Fruto | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Santo Tomás (en) , 16 ga Afirilu, 1991 (32 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Kolombiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mazauni | Santo Tomás (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Yaren Sifen | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 9 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 79 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 178 cm |
Bayan ya fara buga wasa wato aikinsa na ƙwararrun manya tare da ƙungiyar Deportivo Cali ta qasar Colombia, Muriel ya koma Udinese anan qasar italiya wato seria . Shekarunsa biyu na farko a qungiyar din yazama dan wasan shi aro zuwa Granada na qasar spaniya da Lecce a qasar italiya kafin ya koma kulob din a shekarai 2012, a cikin wannan shekarar ya lashe lambar yabo mafi kyawu sosai a matasan na Seria A ta qasar italiya tare da Stephan El Shaarawy . Bayan ya zira kwallaye 15 a wasanni 57, daya buga Muriel ya koma Sampdoria ta Serie A a cikin Janairu 2015. Ya shafe shekaru biyu da rabi tare da kungiyar, inda ya zura kwallaye 21 a wasanni 79 da ya buga kafin ya koma Sevilla a 2017. A cikin Janairu 2019, an mayar da shi Italiya a matsayin aro tare da Fiorentina. A watan Yunin 2019, Muriel ya rattaba hannu a kungiyar Atalanta ta Serie A akan kudi Yuro miliyan 18. A kakar wasansa ta farko, Muriel ya ci kwallaye 18 kuma ya jagoranci Atalanta zuwa matakin cancantar shiga gasar zakarun Turai a karon farko a tarihin kulob din. A kakar wasa ta gaba, ya gama a matsayin na uku saman gola a cikin Serie A, bayan Romelu Lukaku da Cristiano Ronaldo . Sakamakon haka, Atalanta ta cancanci shiga gasar zakarun Turai guda biyu a jere; don ƙoƙarinsa, Muriel ya kasance cikin 2020–21 Seria A Team of the Year .
Muriel a halin yanzu dan kasar Colombia ne kuma dan wasan gaba, wanda ya wakilci al'ummar qasar sa a cikakken matakin kasa da kasa tun shekara ta 2012. Ya buga wasansa na farko a watan Yunin shekarai 2012, a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Ecuador, kuma yazura kwallonsa ta farko a shekarai data gabata mai zuwa, inda ya zura kwallo a ragar Guatemala . Daga baya ya halarci gasar 2015, 2019, da 2021 na Copa América, da kuma 2018 FIFA World Cup .