Mutanen Hamar
From Wikipedia, the free encyclopedia
Al'ummar Hamar (wanda kuma ake yiwa laƙabi da Hamer ) al'umma ce dake zaune a kudu maso yammacin ƙasar Habasha . Suna zaune ne a gundumar Hamer, wani yanki mai albarka na kwarin kogin Omo, a cikin shiyyar Debub Omo na yankin Kudancin Ƙasa, Ƙasa, da Jama'a (SNNPR). Galibinsu makiyaya ne, don haka al’adunsu na ba shanu daraja sosai.