Tamale, Ghana
Birni a Arewa na Ghana. / From Wikipedia, the free encyclopedia
Tamale birni ne mai saurin cigaba a Yammacin Afrika. Shine babban birnin arewacin kasar Ghana. Birnin cibiya ce ta kasuwanci a yankin. Waje ne mai kwanciyar hankali sannan kuma mai sauki wajen kasuwanci. Mutanen birnin mutane ne masu son zaman lafiya. Tamale shine birni na uku mafi girma a kasar Ghana. Yana da yawan jam'a kimanin 950,124 kamar yadda shafin yanar gizo mallakin birnin ya ruwaito. Shine birni mafi saurin cigaba a Yammacin Afrika.[1][2] Birnin na a 600 km (370 mi) north of Accra.[3]
Tamale, Ghana | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | |||
Yankuna na Ghana | Yankin Arewaci | |||
Gundumomin Ghana | Tamale Metropolitan District | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 466,723 (2016) | |||
• Yawan mutane | 622.3 mazaunan/km² | |||
Harshen gwamnati |
Turanci Harshen Dagbani | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 750 km² | |||
Altitude (en) | 151 m | |||
Sun raba iyaka da | ||||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC±00:00 (en)
| |||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | tamale.ghanadistricts.gov.gh |
Mafi akasarin mazauna birnin Tamale Musulmai ne, akwai Masallatai da dama a Tamale, mafiya shahara sune, Masallacin Afa Ajura (masallacin Ambariyyah), da kuma masallatan kungiyar da'awa ta Ahmadiyya.
Tamale na a Arewacin Ghana ne, asalinta daga masarautar Dagbon ta fita. Sarkin shine sarkin al'umar Dagomba wato sarkin Yendi.
Sakamakon kasantuwar Tamale a tsakiya ne yasa birnin yazama matatara ta gudanarwar gwamnati da cibiyar kasuwanci da siyasa a arewacin Ghana.[4]
Cigaban Tamale yazo ne cikin shekaru kadan da suka gabata .[5]