Gwagwarmaya

From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Kokarin kawo Gyara ko sauyi acikin al'umma shine ake kira da Gwagwarmaya.Gwagwarmaya ita ce hanya Mafi sauri da talakawa marasa madafun iko kebi domin neman sauyi da cigaba a cikin al'ummarsu ta hanyar da wasu jajirtattun mutane kefitowa a madadin sauran al-umma danufin neman hakkokin da gobnati ko wasu kungiyoyi suka tauyewa marasa karfi. Dukkan wasu fitattun shugabbanni da ake yabon mulkinsu idan kabi tarihi zaka samu sunfara gwagwarmaya ne misali

  1. Nelson Mandela Afirka ta kudu Wanda yayi yaki da wariyar launin fata akasarsa, sakamakon gwagwarmayarsa yakwato yanci bakaken fata yazama Shugabban kasar bakin fata na farko
  2. Mahatama Ghandi daga India Wanda yayi gwagwarmayarsa akan fafutakar neman yanci daga mulkin mallaka na kasar birtaniya, yayi kokari sosai wajen wanzar da zaman Lafiya da daidaito acikin shugabancinsa bayan karbar mulkin daga turawa.
  3. Kwame Nkurma Kasar Ghana yakasance Daya daga cikin Yan gwagwarmaya aduniya Wanda tarihi bazai manta dasu ba sakamakon kokarinshi wajen nemarwa kasarshi yanci da yunkurin hada kan kasashen Afirka a matsayin kasa guda.
  4. Marthin Luther King Jr. Ba amurke Wanda yayi gwagwarmaya domin Kare haqqin bakar fata da nema musu yanci akasar .
Remove ads
Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads