Hankaka

From Wikipedia, the free encyclopedia

Hankaka
Remove ads

Hankaka wani tsuntsu ne mai dan girma kamar shaho, wanda ke da farin ƙirji sauran jikinsa kuma baƙi. Hankaka bata rayuwa sai inda ke da dogayen bishiyoyi kamar manyan Marake da dogayen giginyu, haka yasa Hausawa ke mata kirari da "Hankaka mai gidan sama"

Quick Facts Conservation status, Scientific classification ...
Thumb
hankaka asama
Thumb
hankaka visa itace
Thumb
Thumb
Hankaka bisa benci
Thumb
hankaka bisa kwakwa
Thumb
hankaka yana koto
Remove ads

YADDA HANKAKA YAKE YADUWA

Asalin yadda hankaka yake yin karuwa shine, kamar kowanne Tsuntsu shima hankaka macen tana yin kwai ne kamar guda uku zuwa shida. Sannan kuma sai tayi kwanci daganan ta kyankyashe. Bahaushe yace "hankaka maida dan wani naka", wannan karin maganar wani hasashe ne na malam bahaushe dan yana ganin hankaka kandauki kwai na Kaza ko na Agwagwa ko gunya ko ma mai kyau ya tashi yayi sama dashi. To me yake dashi? shidai wannan kwan hankaka yana kaishi ne can kan shekar shi inda macen ke kwanci, daidai lokacin da zata kyankyashe ne kuma wannan kwan da namijin hankaka ya dauko shima kuma ya rube, shine zai zama abincin yan tsakin hankakin.

Remove ads
Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads