Wake
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Wake irin tsire-tsire ne da ke cikin dangin Fabaceae, wanda ake nomawa domin abinci da kuma wasu dalilai na rayuwa. Wake na ɗaya daga cikin manyan tsaba-tsaba masu ɗauke da furotin mai yawa, kuma ana amfani da shi a ƙasashe da dama wajen sarrafa abinci iri-iri. Ana iya dafawa, soyawa, ko kuma niƙa wake a matsayin gari. Haka kuma, wake na ɗaya daga cikin abinci mafi sauƙin samu da ciyar da jama'a a faɗin duniya, musamman a Afirka da Asiya.
Remove ads
Iri
Akwai ire-iren wake da dama da ake nomawa a duniya, ciki har da:
- Farin wake
- Jan wake
- Baƙin wake
- Wake mai launin ruwan ƙasa
- Wake mai launin kore
Wasu daga cikin irin wake da ake nomawa a Najeriya sun haɗa da:
- Waken hausa (cowpea – Vigna unguiculata)
- Waken filawa
- Wake ganye
Muhimmanci
Wake na da muhimmanci sosai a cikin abinci saboda yana ƙunshe da furotin, sinadirai masu gina jiki, da kuma ƙarancin kitse. A ƙasashe masu tasowa, wake na taka muhimmiyar rawa wajen rage yunwa da samar da abinci mai arha ga talakawa. A Najeriya, ana amfani da wake wajen dafa abinci kamar:
- Moi-moi (wake da aka nika dafa shi da kayan miya)
- Akara (wake da aka nika aka soyashi)
- Danwake
- Waina wake
- Tuwo da wake
Remove ads
Noma
Ana nomar wake a ƙasashe da dama, musamman a yankunan da ke da ƙarancin ruwa. Wake na iya girma a ƙasa mara kyau saboda yana iya ɗaukar nitrogen daga iska. A Najeriya da yawancin ƙasashen Afrika, ana dasa wake bayan an girbi hatsi kamar dawa ko masara.
Hotuna
- Farin Wake
- Dafaffar Shinkafa da Wake
Manazarta
- National Research Council (2006). Lost Crops of Africa: Volume II: Vegetables. National Academies Press. ISBN 978-0-309-10333-6.
- Duke, James A. (1981). Handbook of Legumes of World Economic Importance. Springer. ISBN 978-1-4684-8151-3.
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads