Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Togo
From Wikipedia, the free encyclopedia
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo, tana wakiltar Togo a wasannin ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa kuma hukumar kula da wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo ce ke tafiyar da ita. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo ta fara shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekara ta 2006. Motar tawagarsu ta fuskanci wani mummunan hari a Angola kafin gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2010 . Sun janye daga gasar kuma daga bisani hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta dakatar da su daga shiga gasar. A shekara ta 2013 a karon farko a tarihi, Togo ta kai wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Afrika . Tawagar tana wakiltar duka FIFA da kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).