Akbar Hashemi Rafsanjani
From Wikipedia, the free encyclopedia
Akbar Hashemi Rafsanjani (Persian: اکبر هاشمی رفسنجانی, an haife shi a ranar 25 ga watan Agustan 1934 kuma ya mutu a ranar 8 ga watan Janairun 2017) Dan siyasa ne a kasar Iran, marubuci ne kuma daya daga cikin jiga jigan juyin juya hali na kasar kasar ta Iran. Wanda shine shugaban kasa na hudu daga 1989-1997 a shuwagabannin kasar bayan tabbatar da Gwamnatin musulunci. Shine shugaban kwararru masu kafa doka a iran wato Assembly of Experts tun daga 2007 har zuwa 2011 a lokacin da kansa yaji bashida muradin zama a wannan matsayin[1][2]
Akbar Hashemi Rafsanjani | |||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
25 ga Yuli, 2007 - 8 ga Maris, 2011 ← Ali Meshkini (en) - Mohammad-Reza Mahdavi Kani (en) →
4 Oktoba 1989 - 8 ga Janairu, 2017 ← Ali Khamenei - Mahmoud Hashemi Shahroudi (en) →
17 ga Augusta, 1989 - 2 ga Augusta, 1997 ← Ali Khamenei - Mohammad Khatami →
15 ga Augusta, 1983 - 8 ga Janairu, 2017
28 ga Yuli, 1980 - 3 ga Augusta, 1989 ← Javad Saeid (en) - Mehdi Karroubi (en) →
28 Mayu 1980 - 3 ga Augusta, 1989 District: Tehran, Rey, Shemiranat and Eslamshahr (en)
6 Nuwamba, 1979 - 12 ga Augusta, 1980 ← Hashem Sabbaghian (en) - Mohammad-Reza Mahdavi Kani (en) → | |||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||
Haihuwa | Nuq District (en) da Bahreman (en) , 25 ga Augusta, 1934 | ||||||||||||||
ƙasa | Iran | ||||||||||||||
Mutuwa | Tehran da Tajrish (en) , 8 ga Janairu, 2017 | ||||||||||||||
Makwanci |
Behesht-e Zahra (en) Khomeini Mausoleum (en) | ||||||||||||||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon zuciya) | ||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||
Abokiyar zama | Effat Marashi (en) (1958 - | ||||||||||||||
Yara | |||||||||||||||
Ahali | Mohammad Hashemi Rafsanjani (en) | ||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||
Makaranta |
University of Qom (en) University of Isfahan (en) University of Tehran (en) | ||||||||||||||
Harsuna | Farisawa | ||||||||||||||
Malamai | Hussein-Ali Montazeri (en) | ||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, marubuci, entrepreneur (en) da akhoond (en) | ||||||||||||||
Kyaututtuka | |||||||||||||||
Aikin soja | |||||||||||||||
Fannin soja | Armed Forces of the Islamic Republic of Iran (en) | ||||||||||||||
Ya faɗaci | Iran–Iraq War (en) | ||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||
Addini | Shi'a | ||||||||||||||
Jam'iyar siyasa | Executives of Construction Party (en) | ||||||||||||||
A cikin shekaru 40 da ya yi yana mulki, Rafsanjani ya tara dimbin madafun iko wanda ya zama kakakin majalisar dokoki, babban kwamanda a lokacin yakin Iran da Iraƙi, sannan ya zabi Ali Khamenei a matsayin shugaban koli na Iran. Matsayinsa mai karfi da iko a kan siyasar Iran ya sa aka ba shi suna Akbar Shah[3][4]
Rafsanjani ya zama shugaban kasar Iran bayan ya lashe zaben 1989. Ya sake yin wani wa’adin mulkin bayan daya kara lashe zaben shekarar 1993. A zaben 2005 ya sake tsayawa takara karo na uku, inda ya zo na daya a zagayen farko na zaben amma a karshe ya sha kaye a hannun abokin hamayyarsa Mahmoud Ahmadinejad a zagaye na biyu na zaben. Shi da iyalinsa sun fuskanci keɓewar siyasa saboda goyon bayan da suka bai wa 'yan adawa a shekarar 2009. Rafsanjani ya kara shiga takarar neman shugabancin ƙasar a shekarar 2013[5] amma Majalisar ta hana shi takara.Da zaben Hassan Rouhani, wanda Rafsanjani ya fito fili ya goyi bayansa, a hankali dangin Rafsanjani sun dawo da martabarsu a siyasance. Rafsanjani ya mutu a cikin 2017, sakamakon bugun zuciya, a wani asibiti a Tehran yana da shekaru 82.[6][7][8] Duk da cewa jami'an gwamnati sun danganta mutuwarsa da bugun zuciya, mutuwarsa ta kwatsam ta sa ake rade-radin cewa an kashe shi. Iyalinsa sun tabbatar da cewa an kashe shi akayi. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa jikinsa na dauke da sinadarai masu aman guba wato radioactive.