Dajin yanayi na Vatican
From Wikipedia, the free encyclopedia
Gidan dajin Yanayi na Vatican,wanda zai kasance acikin Bükk National Park, Hungary,an bada gudummawa ga Vatican City ta hanyar kamfanin carbon. Za'a dai-daita gandun dajin don rage fitar da hayaƙi na carbon da Vatican ta samar acikin shekara ta alif dubu biyu da goma sha bakwai 2007. Amincewar Vatican game da tayin, a wani bikin a ranar biyar 5 ga watan Yuli, shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2007,an ruwaito shi a matsayin "alamu ne kawai", kuma hanya ce ta ƙarfafa Katolika suyi ƙarin don kare duniya.[1] Babu bishiyoyi da aka dasa a ƙarƙashin aikin kuma ba'a samar da carbon ba.[2][3]
Dajin yanayi na Vatican | |
---|---|
daji | |
Bayanai | |
Ƙasa | Hungariya |
Mamallaki | Cocin katolika |
Acikin wani yunkuri mai tasiri don yaki da dumamar yanayi, a watan Mayu na shekara ta alif dubu biyu da bakwai 2007, Vatican ta bada sanarwar cewa za a rufe rufin Paul VI Audience Hall da bangarorin photovoltaic. An sanya shigarwar a hukumance a ranar ashirin da shida 26 ga watan Nuwamba, shekarar alif dubu biyu da takwas 2008.