Kisan kiyashi a Odi
Sojoji sun kai hari a garin Odi na Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Kisan kiyashin Odi[1][2] wani hari ne a ranar 20 ga watan Nuwamba, 1999 da sojojin Najeriya suka kai a wani garin Odi da ke jihar Bayelsa mafi rinjayen kabilar Ijaw.[3] Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe tashen hankula a yankin Neja-Delta[4] kan haƙƙin ƴan asalin ƙasar mai albarkatun mai da kuma kare muhalli.[5] An kiyasta cewa an kashe fararen hula sama da 900 a harin.
Quick Facts Iri, Kwanan watan ...
| |
Iri |
aukuwa Kisan Kiyashi |
---|---|
Kwanan watan | 20 Nuwamba, 1999 |
Wuri | Bayelsa |
Ƙasa | Najeriya |
Kulle
Jama'a dai na cewa gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ne suka bada umarnin kisan kiyashi.[2] Sojoji sun sha kare matakin da suka dauka inda suka ce an yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa Odi. Hakan ya sa tashin hankali ya tashi kafin shiga kauyen.