![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/8b/Kairo_Al_Hussein_Mosque_BW_1.jpg/640px-Kairo_Al_Hussein_Mosque_BW_1.jpg&w=640&q=50)
Masallacin Hussaini
From Wikipedia, the free encyclopedia
Masallacin al-Hussain ko masallacin al-Husain,[1][2] wanda kuma aka fi sani da masallacin al-imam al-Husayn[3][4] ( Larabci: مسجد الإمام ٱلحُسين) da masallacin Sayyidna al-Husayn masallaci ne kuma makabartar Husaini bn Ali, wanda aka gina shi a shekara ta 1154, sannan aka sake gina shi a shekara ta 1874.[5] Masallacin yana a birnin Alkahira na kasar Masar, kusa da kasuwar Khan El-Khalili, kusa da shahararren masallacin Al Azhar, a wani yanki da ake kira Al-Hussain.[4] Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin wurare masu tsarki na Musulunci a Masar. Wasu musulmin Shi'a sun yi imanin cewa an binne kan Hussaini ( ra's mubarak ) a harabar masallacin da ke a yau wani makabarta kuma ana daukarsa a matsayin abin da ya rage na gine-ginen Fatimid da ke cikin ginin.
Masallacin Hussaini | |
---|---|
![]() | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Misra |
Governorate of Egypt (en) ![]() | Cairo Governorate (en) ![]() |
Coordinates | 30°02′52″N 31°15′47″E |
![]() | |
Suna | AlHusain dan Aliyu bin Abi Talib |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) ![]() |
Islamic architecture (en) ![]() |
|