CNN
From Wikipedia, the free encyclopedia
CNN (Cable News Network) tashar watsa labarai ce ta ƙasa da ƙasa mai hedikwata a Atlanta, Jojiya, Amurka.[1][2][3] An kafa ta a cikin shekarata 1980 ta hannun mai mallakar kafofin watsa labarai na Amurka Ted Turner da Reese Schonfeld a matsayin tashar watsa labarai na tsawon sa'o'i 24 a kullum, kuma a halin yanzu mallakar kamfanin na watsa labarai na hannun Manhattan, Warner Bros. Discovery.[4] CNN ita ce tashar talabijin ta farko da ta fara watsa labarai tsawon sa'o'i 24. Kuma tashar talabijin ta farko- da ta fara watsa labarai a Amurka.[5][6][7][8][9]
URL (en) | https://www.cnn.com/ |
---|---|
Iri | United States cable news (en) , specialty channel (en) , news website (en) da film production company (en) |
Slogan (en) | Go There, This is CNN, More People Get Their News from CNN From Any Other Source, The World's Most Trusted Name in News, The Most Trusted Name in News, The Worldwide Leader in News, Facts First, Reporting From Around the World, The World's News Network da The World's News Leader |
Bangare na | WarnerMedia (en) |
Mai-iko | Warner Bros. Discovery (en) |
Maƙirƙiri | Ted Turner (en) da Reese Schonfeld (en) |
Service entry (en) | 1 ga Yuni, 1980 |
Wurin hedkwatar | CNN Center (en) da New York |
Wurin hedkwatar | Tarayyar Amurka |
Kyauta ta samu | Peabody Awards (en) , Princess of Asturias Award for Communications and Humanities (en) , Golden Nymph for Best 24-Hour News Program (en) , Four Freedoms Award – Freedom of Speech (en) , George Polk Award (en) , Four Freedoms Award (en) , News and Documentary Emmy Award (en) da Walter Cronkite Award for Excellence in Journalism (en) |
CNN, CNNOriginals, cnnbrk, CNNPolitics, cnni, cnnweather da CNNPR | |
cnn | |
cnn | |
Youtube | UCupvZG-5ko_eiXAupbDfxWw |
Tun daga watan Satumba na shekarar 2018, CNN tana da masu mu'amala (subscribers) da tashar mutane miliyan 90.1 a matsayin masu biyan kuɗi (subscriptions), kuma (kashi 97.7% cikin 100 na masu mu'amala da tashar, na da tashar acikin akwatunan telebijin nasu a gidajen su).[10] MSNBC, matsakaicin masu kallo 580,000 a ko'ina cikin yini, ya ragu da kashi 49% daga shekarar da ta gabata, a cikin raguwar masu kallo a duka hanyoyin sadarwar tashar (channels).[11] Yayin da CNN ke a matsayi na 14 a cikin jerin tashoshin watsa labarai a shekara ta 2019,[12][13] gidan telebijin ɗin yayi kukan kura inda ya zabura izuwa mataki na 7th daga mataki na 14 da yake abaya. Acikin manyan hanyoyin sadarwa da sukayi fice akwai; (Fox News a mataki na 5, da MSNBC a mataki na 6, a wannan shekarar),[14] ta koma mataki na 11 a shekarar 2021.[15]
A duk duniya, shirye-shiryen CNN ana watsawa ta hanyar CNN International, waɗanda masu kallo ke gani a cikin ƙasashe da yankuna sama da 212;[16] tun daga watan Mayu 2019. Gidan talabijin ɗin mallakar Amurka, ana takaita sunan da CNN (US), Bugu da ƙari tana watsa shirye-shiryen ta a Kanada, wasu tsibiran Caribbean da kuma a Japan, inda aka fara watsa shirye-shirye a kafar yaɗa labarai ta CNNj a shekara ta 2003, tare da fassarar lokaci guda cikin harshen Jafananci.[17]