![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/2/28/Nigeriahouseofreps.jpg/640px-Nigeriahouseofreps.jpg&w=640&q=50)
Gwamnatin Tarayyar Najeriya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Gwamnatin tarayyar Najeriya tana da rassa guda uku: 'yan majalisu, zartaswa, da shari'a, wadanda kundin tsarin mulki ta ba su iko daga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya a Majalisa da shugaban kasa da kotunan tarayya ciki har da kotun koli. Kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi rarrabuwa mukamai da daidaito a tsakanin bangarorin guda uku da nufin hana maimaita kura-kuran da gwamnati ta yi a baya.[1][2]
![]() | |
---|---|
political system (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Shafin yanar gizo | nigeria.gov.ng |
Najeriya jamhuriya ce ta tarayya, wacce shugaban kasa ke da ikon zartarwa. Shugaban kasa shi ne shugaba a kasa, jagoran gwamnati, kuma shugaban tsarin jam’iyyu da yawa. Siyasar Najeriya tana gudana ne a cikin tsarin tarayya, shugabancin kasa, jamhuriya dimokuradiyya mai wakilci, inda gwamnati ke amfani da ikon zartarwa. 'Yan majalisa na karkshin gwamnatin tarayya da kuma majalisun dokoki guda biyu: majalisar wakilai da ta dattawa. A dunkule, majalisun biyu su ne hukumar da ke kafa doka a Najeriya, wadda ake kira majalisar dokokin kasar, wadda ke zaman tantance bangaren zartarwa na gwamnati.[3] "Economist Intelligence Unit" ya kimanta Najeriya a matsayin "hybrid regime" " a shekara ta 2019.[4] Gwamnatin Tarayya, Jihohi, da Kananan Hukumomin Najeriya na da burin yin aiki tare domin gudanar da mulkin kasa da al’ummarta.[5] Najeriya ta zama mamba ja kungiyar Commonwealth ta Burtaniya bayan samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta 1960.[6]