Koh-i-Noor
From Wikipedia, the free encyclopedia
Koh-i-Noor (ana kuma furta Koh-i-Nûr da Kooh-è Noor, kokuma Kohinur a furucin Hausa) wani babban zinare ne mai darajar gaske da aka sameshi a garin Guntur na jahar Andhra Pradesh kasar Indiya, a karni na goma sha uku.[1] Ma'anar sunan shine Hasken Tsauni a harshen Pashiya.
![]() | |
---|---|
diamond (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Bangare na |
Crown Jewels of the United Kingdom (en) ![]() |
Color (en) ![]() | Fari |
Location of discovery (en) ![]() |
Kollur Mine (en) ![]() |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/3/31/Koh-i-Noor_old_version_copy.jpg/640px-Koh-i-Noor_old_version_copy.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/01/Koh-i-Noor_new_version_copy.jpg/640px-Koh-i-Noor_new_version_copy.jpg)
Kafin a yanke shi, nauyinsa yakai giram 793. Daular Kakatiya ce farkon mamallakiyar zinaren. Daga baya mallakin zinaren ya sauya zuwa hannayen daban-daban a yankin Kudancin Asiya. Karshe dai zinaren Koh-i-Noor ya karkare ne a hannan sarauniya Victoria bayan Birtaniya ta karbe iko da yankin Punjab a 1849. A yanzu zinaren a ikon Birtaniya ne.[2]
Tun baya bayyanar sa a Birtaniya zinaren yakasance ne a karkashin ikon matayen dake sarautar masarautar ta Birtaniya,[3] ya fara ne daga hannun Sarauniya Victoria. Bayan rasuwar Victoria sai Koh-i-Noor yakoma hannun Sarauniya Alexandra, matar Edward VII. Daga nan sai zinaren ya koma hannun Sarauniya Mary a 1911,[4] daga karshe zinaren ya koma hannun Sarauniya Elizabeth 1 a 1937.[5] Bayan rasuwar ta a 2002, yanzu zinaren yana karkashin ikon ma'ajiyar zinare ta Birtaniya. Kowacce shekara miliyoyin masu ziyara ne ke zuwa kallon shi.