Masallacin Omar Ibn Al-Khattab
From Wikipedia, the free encyclopedia
Masallacin Omar Ibn Al-Khattab ( fassarar Spaniyanci Omar Iban Al-Jattab ) masallaci ne a Maicao, La Guajira, a Kasar Colombia. Shi ne masallaci na uku mafi girma a Latin Amurka. Ana kiran shi kuma da "La Mezquita" ("Masallacin"), saboda shine masallaci tak a yankin. Tare da Makarantar Dar Alarkan, su ne cibiyoyin addinin Musulunci da al'adunsu a yankin. An gina masallacin a ranar 17 ga watan Satumban 1997, kuma an sa masa suna bayan halifan Sunni na biyu Omar Ibn Al-Khattab .[1] Masanin gine-ginen na kasar Iran Ali Namazi ne ya zana masallacin, wanda injiniyan gine-gine Oswaldo Vizcaino Fontalvo ya gina, ta amfani da marmara ta Italiya don gina ta. Zai iya ɗaukar mutane aƙalla sama da mutum dubu ɗaya.
Quick Facts Wuri, Coordinates ...
Masallacin Omar Ibn Al-Khattab | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Kolombiya |
Department of Colombia (en) | La Guajira Department (en) |
Municipality of Colombia (en) | Maicao (en) |
Coordinates | 11°22′41″N 72°14′04″W |
History and use | |
Opening | 1997 |
Ƙaddamarwa | 17 Satumba 1997 |
Suna saboda | Sayyadina Umar |
Addini | Musulunci |
Suna | Sayyadina Umar |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Tsawo | 31 m |
Offical website | |
|
Kulle