Adebola Williams
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Adebola Williams (An haife shi a shekara ta 1986) dan kasuwa ne na kafofin watsa labarai dan Najeriya, ɗan jarida, mai bada shawarwarin siyasa kuma mai jawabin kara karfin gwiwa. Shine CED na RED I For Africa, Ya mika ragamar shugabancin ga Ayodeji Razaq a cikin shekara ta 2022.[1] Tare da shi aka kirkiri Red Africa kuma ya jagorance ta. Kungiya mafi girma ta matasa 'yan midiya wanda ya hada da Red Media Africa, Statecraft Inc., The Future Awards Africa, and YNaija.[2]

Aikinsa na watsa labarai da talabijin ya fara ne a Hukumar Talabijin ta Kasa (NTA) tare da ba da shawara ga matasa, daga karshe kuma shugabanci mai kyau. Nana Akufo-Addo ya suffantashi a matsayin "mutum mai sa’a" a duk abubuwan ya sa gaba. Forbes ta bayyana shi a matsayin mutumin da ya taimaka wajen zabar shugabannin kasa a Africa ta hanyar cinke.[3]Samfuri:Self-published inline
Remove ads
Kuruciya
An haifi Williams 7 ga watan Maris 1986 "ga dangi attajiraii, amma lokacin yana ɗan shekara 10, danginsa sun rasa duk abin da suke da shi don haka dole ya sha gwagwarmaya."[4] A farkon shekarunsa na matashi, Williams yana son zama ɗan wasan kwaikwayo kuma an biya shi cent 50 kawai don rawar da fara takawa a wasan kwaikwayo.[5]
Ya fara aiki a matsayin mataimaki tare da mai ba da shawara da masanin ilimin halayyar dan adam a matsayin mai aikin yanar gizo tare da wani cikakken ililmi ba a yayinda a lokacin ya shafe shekaru 3 yana gogewa tare da Hukumar Talabijin ta Kasa (NTA).[4]
Remove ads
Sana'a
Williams da Chude Jideonwo sun fara aiki da The Future Awards Africa sannan suka ci gaba da haɗa gwiwa wajen kirkirar Red Media Africa.[6]
AN kafa EnoughisEnough (EiE) tare da shi, wani shafi na shigar jama'a 'yan Najeriya da murya ga matasa a harkar siyasa.[7] Ya yi murabus a matsayin shugaban hukumar don jan ragamar tsarin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, inganta aikin kafofin watsa labarai don canza hasashe na dindindin da janyo hankali kan zabe.[8] Nasarar da aka samu a Ghana ta taimaka wa ɗan takarar adawa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a yunƙurinsa na uku, kuma a halin yanzu Williams yana bada shawarwari a wasu yankuna na nahiyar.
Yawon bada shawarwarinsa na 2017 ya hada da taruka daban daban a Makarantun ivy league Harvard, Columbia, da kuma Oxford.[9] Ya bada jawabi a wajen Torn Obama na shekara ta 2017 a Chicago.[10]
Aikinsa a kasuwancin kamfani da maganganunsa sun shafi harkokin mai da gas, zuwa harkokin banki, da fasaha, da kayan amfanin yau da kullum da ke shiga cikin sauri, sun samar masa da kamfanin RED Africa Lambobin yabo da dama a nahiyar daga lambobin yabo na SABRE,[11] Lapriga,[12] Marketing Edge, Young Cannes da kuma kyautuukan C4F Marketing a Davos.[13] Yana rubuta labarai a duk wata ga kamfanoni da kafafen sadarwa a jaridar The Guardian (Najeriya).[14] Williams ya sanya hannu wajen assasa babban hadin gwiwa na wani zane mai suna Remember To Rise.[15]
Ya bada jawabi a wajen taron Afurka ta European Conservatives and Reformists (ECR) Africa Summit aa ranar Laraba, 9 Junairun 2019, a Majalisar Turai a kan dimukradiyya da shugabanci mai kyau.[16]
Remove ads
Karramawa
- Mandela Washington Fellowship, Shirin Shugabannin Matasan Afirka, haɗin gwiwa don yin karatu a Amurka tsawon makonni shida[17]
- 2014: Abokin nasara tare da Chude Jideonwo, Jagoran Matasa 'yan Kasuwa na Shekara, Afirka ta Yamma, CNBC Africa All Africa Business Leaders Awards 2014[18]
- 2017: EMY Ghana ta sa masa suna Matahi Mai Nasara daga Afurka[19]
- 2017: An sanya masa suna ɗaya daga cikin Manyan mutane 100 masu tasiri na zuriyar Afirka a ƙarƙashin shekaru goma na Majalisar Dinkin Duniya na mutanen asalin Afirka
- 2018: Archbishop Desmond Tutu Fellowship a Afirka ta Kudu
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads