Aleiro
Karamar hukuma ce a garin kebbi stet, a najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Aleiro karamar hukuma ce dake a Jihar Kebbi, Arewa maso yammacin Nijeriya, helkwatar ta tana cikin garin aleiro sunan shugaban karamar hukumar Alhaji shu'aibu Ibrahim . Yana da fadin fili na kilomita murabba’i 350 kuma yana da yawan jama’a da suka kai 65,973 a ƙirgar ƙidayar jama’a ta shekarar 2006.
Lambar gidan waya ta yankin ita ce 863.[1]
Remove ads
Fage
Asalin Aliero na iya komawa tun ƙarshen ƙarni na 16, lokacin da kabilun Namasawa da Kabawa suka kafa garin. A ƙarni na 17, yawan jama’ar Aliero ya karu yayin da mutane daga kabilu daban-daban, kamar su Bare-bare daga Barno, Marina daga ƙasar Nupe, Zamfarawa daga Zamfara, da Wangarawa daga Mali, suka ƙaura zuwa yankin kuma suka zauna a nan saboda ƙasar da take da albarka.
Sunan "Aliero" ya samo asali ne daga wani makiyayi dan kabilar Fulani mai suna Ali Dan Yaro, wanda ke kawo dabbobinsa duk shekara don kiwo a yankin Zauro/Ambursa, inda yake zama na ɗan lokaci. Sunan ya rikide daga "Ali Yaro" zuwa "Aliero" ne a zamanin mulkin mallaka na Birtaniya.
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads