Apapa

karamar hukumace a jahar lagos najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia

Apapa
Remove ads

Apapa Karamar hukuma ce da take a yammacin tsibirin Lagos a Jihar Lagos, Nijeriya. A cikin Apapa akwai tashoshin jiragen ruwa da dama kuma suna gudanar da ayyukansu a karkashin Nigerian Port Authority (NPA) wanda suka hada da aininhin tashar jiragen ruwa na Lagos da kuma tashar Lagos Port Complex (LPC).[1]

Quick Facts Wuri, Yawan mutane ...
Thumb
Apapa logos
Thumb
Tashan Jirgin RUWAN Apapa
Thumb
Apapa Water
Remove ads

Bayani

Karamar hukumar Apapa tana nan kusa da tafkin Lagos (watau Lagos Lagoon), sannan kuma akwai nau'ikan kaya kala kala kaman kwantenoni da cargo-cargo, gidaje, ofisoshi da wata tsohuwar titin jirgin kasa wacce bata aiki a yanzu a arewacin Apapa. Itace kuma ainihin kafar shigo da kayayyaki na Najeriya har zuwa 5 ga watan Mayun shekara ta 2005 lokacin da ta koma karkashin kungiyar sufuri ta ruwa watau Danish firm A. P. Moller-Maersk Group. [2]Sannan daura da wannan tashar akwai tashar jiragen ruwa na Tin Can Island Port (TCIP).[3]

Har wayau akwai matatan man-fetur a cikin Apapa kamar Bua Group. Sannan akwai ofisoshi manymanya na kasuwanci sufurin kaya zuwa wurare daban daban a duniya. Daga cikin sanannun gine-gine akwai Folawiyo Towers. Acikin Apapa akwai hedikwatoci da dama kamar hedikwatan gidan jarida na Najeriya watau Thisday.[4]

Remove ads

Tarihi

Thumb
Apapa

An tsinci wani sarakar tagulla a karni na 16 wanda a yanzu haka yana nan a jiye a gidan tarihi na British Museum. Acikin shekara ta 2015 aka kaddamar da aikin ginin gidajen zamani a fili me fadin eka 1000. An kammala aikin ginin a tsakanin shekarun 1957/1958 kuma ta wanzu tare da fadada Apapa Wharf. Gidajen sun kunshi tarin ma'aikatan kamfanoni musamman na gine-gine da sauransu. Makarantar German School Lagos tana Apapa a da.[5]

Remove ads

Gidajen da kayan Gwamnati

Gidaje da wuraren karatu

A cikin Apapa akwai gidaje iri-iri kama daga na alfarma masu tsada har da matsakaita tsada da saukin kudi.[6]

Thumb
Apapa

Akwai wuraren shakatawa iri-iri kamar wurin hawa jirgin ruwa na zama a Apapa Creek.

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads