Charanchi

Karamar hukuma ce a jihar Katsina, Nigeria From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Charanchi (ko Cheranchi ) ƙaramar hukuma ce a jihar Katsina, arewacin Najeriya. Garin, akan babbar hanyar A9, shi ne hedkwatar karamar hukumar.[1]Shugaban karamar hukumar shine Dr.Badamasi Lawal Charanchi[2] yawan jama'a ya kai kimanin 79,000 (2003), kuma yankin ya kai 471. 2. [1]

Quick facts Wuri, Yawan mutane ...
Remove ads

Tarihi

An kafa karamar hukumar ne daga tsohuwar karamar hukumar Rimi a shekarar 1996. A yanzu haka akwai kansiloli 11 da ke wakiltar mazabarsu a harkokin gudanarwar karamar hukumar. Wadannan kansilolin suna da hakkin tsige Shugaban Karamar Hukumar idan aka yi rashin da’a ko almubazzaranci da asusun gwamnati.

Hakimi

Akwai hakimai biyu a karamar hukumar; Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanchi da Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye.

Sauran garuruwa

Sauran garuruwan karamar hukumar sun hada da Kuraye, Banye, Radda, Koda, Ganuwa, Yana, sabon Gari da Maje.

Manazarta

Hanyoyin haɗi na waje

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads