Emeka Offor
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Emeka Offor (an haife shi a ranar 10 ga watan Fabrairu, 1959) hamshakin attajiri ne, mai ba da taimako kuma ɗan kasuwa. Shi ne tsohon shugaban Erhc Energy Inc, Shugaba na Chrome Group, daya daga cikin manyan kamfanonin mai da iskar gas a Afirka ta Yamma, kuma wanda ya kafa gidauniyar Sir Emeka Offor.[1]
Remove ads
Fage
Offor ya fito ne daga Irefi Oraifite a karamar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra, Najeriya. Offor ya yi karatun firamare a makarantar firamare ta Eziukwu da ke Aba, jihar Abia, da kuma makarantar firamare ta St. Michael da ke Ogbete, Enugu. Bayan kammala karatunsa na firamare, ya fara karatunsa na sakandare a Makarantar Merchant of Light, sannan ya koma Abbot Boys High School, Ihiala, Jihar Anambra. [2] Shi Knight ne na Saint Christopher a cikin Cocin Najeriya,[3] kuma daya daga cikin firimiya Knights a Oraifite, Jihar Anambra.
Remove ads
Tallafawa
Ya kirkiro gidauniyar Sir Emeka Offor (SEOF) "domin taimakawa mutanen da suke bukata su zama masu zaman kansu da dogaro da kansu".[4][5]
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads