Kingsley Ogoro

From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Kingsley Eloho Ogoro (an haife shi a watan Agusta 29, 1965), darektan fina-finan Najeriya ne, marubucin allo, furodusan kiɗa kuma tsohon ɗan rawa. Ya yi fice a fim din Osuofia a shekarar 2003 da aka yi a Landan tare da Nkem Owoh, kuma tun daga nan ya fara aiki a matsayin furodusa da darakta a masana’antar fina-finan Nollywood.

Quick facts Rayuwa, Haihuwa ...
Remove ads

Rayuwar farko

Ogoro ya halarci Jami’ar Sakkwato inda ya karanta Banki & Finance, inda ya kammala a shekarar 1988, amma ya ci gaba da sha’awar waka duk da rashin amincewar iyayensa. Kafin karatunsa na jami'a, ya kai wasan karshe na John Player Disco Dancing Championship, bayan haka ya fara mai da hankali kan aikin kiɗa a matsayin furodusa.[1]

Rayuwa ta sirri

A baya dai Ogoro ya auri tsohon mawakin Fafa Esse Agesse. Diyarsu, Ewoma, ita ce Miss Nigeria Ireland a 2012.[2]

Sana a

Shirya fim

Bada umarni

  • The Widow (2005)
  • Osuofia in London 2 (2004)
  • Veno (2004)
  • Osuofia in London (2003)
  • The Return (2003)

Marubuchi

  • The Widow (2005)
  • Osuofia in London 2 (2004)
  • Osuofia in London (2003)

Duba kuma

  • List of Nigerian film producers

Manazarta

Hanyoyin hadi na waje

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads