Musawa
Karamar hukuma a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Musawa karamar hukuma ce a jihar Katsina a Najeriya . Hedikwatarta tana cikin garin Musawa. Musawa na ɗaya daga cikin tsofaffin kananan hukumomi guda bakwai (7), wadanda aka kirkira bayan da katsina ta samu jaha. Wadannnan kananan hukumomi sun haɗa da: Funtua, Malunfashi, Mani, Dutsen ma, Musawa, Daura da kuma ita kanta Katsina. Musawa na da kasuwa guda ɗaya wadda take ci a duk ranar Asabar da Laraba. Mutanen garin Musawa suna kasuwanci da noma, Kuma suna karatu na addini dana zamani. A kwanan nan aka bada mukamai masu girma a garin Musawa wadanda suka haɗa da Hannatu Musa Musawa wadda aka baiwa mukamin minista, Hadiza Bala Usman itama an bata mukamin mai baiwa shugaban ƙasa shawara, sai Zainab Musa Musawa wadda aka baiwa kwamishina a jihar Katsina. Garin Musawa yana da yawan matasa sosai sai dai basu cika yin karatu mai zurfi ba, duk da yawan manyan mukaman da ake baiwa 'yan garinsu. Garin Musawa na da masallatan juma'a guda uku (3), inda bangaren izala ke da guda biyu (2) bangaren darika ke da guda ɗaya (1). Suna masallatan Khamsus Salawat da yawa a Kowane bangare. Garin Musawa na da yanki na 849 km2 da yawan jama'a 171,714 a ƙidayar shekara ta 2006.



Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 833.[1] Garin Musawa Yana da tsohon tarihi Kuma suna da manyan mutane irin sure Alh. Musan Musawa, Alh. Dr. Bala Usman, Alh Abdullahi Dikko Inde da dai sauransu.
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads