Niger State Polytechnic

From Wikipedia, the free encyclopedia

Niger State Polytechnic
Remove ads

Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Neja, Wanda aka fi sani da Niger poly, babbar makarantar koyarwa ce dake a Zungeru, Jihar Neja, Nijeriya.

Quick Facts Bayanai, Iri ...
Thumb
Thumb
Dorben.Polytechnic_Cafeteria_13
Thumb
Dorben.Polytechnic_SIgnpost_16
Thumb
hoton niger polytechnich

Tarihi da manufa

Cibiyar ta fara ne a matsayin Kwalejin Ilimi ta Zungeru (ZUCAS). Gwamnatin jihar ta kafa ZUCAS tare da Dokar Jihar Neja a shekara ta 1979 mai lamba 7, kodayake a zahiri ta fara aiki ne a ranar Goma ga watan Janairu shekara ta 1977 a wani wurin wucin gadi a Kwalejin Gwamnati, a Bida . A watan Satumba na shekara ta 1984 ma'aikatar ta koma matsayinta na dindindin wanda ke tsakanin Zungeru da Wushishi . Manufofin kwalejin shi ne samar da karatuttukan asali don shirya ɗalibai don buƙatun shiga jami'a, da ba da kwasa-kwasai a matakin ƙaramin digiri. Tsarin Ilimi na 6-3-3-4 a cikin Najeriya ya buƙaci a sake maimaita shi da daidaita yanayin matsayin Makarantun Kwalejin Nazarin Asali da Makarantun Koyon Ilimin Gaba. Ganin haka, sai gwamnatin jihar Neja ta hanyar Kammalawa mai lamba C 4 (11) ga Disamba 1990, ta amince da sauya ZUCAS zuwa (Niger State Polytechnic Zungeru). Bayan haka, Dokar Jihar Neja mai lamba Tara a shekara ta 1991 aka fara aiki daga daya ga watan Oktoba shekara ta 1991 don tallafawa.

Polytechnic yanzu tana aiki da tsarin kwaleji tare da manyan cibiyoyi biyu: Kwalejin Kimiyya da Fasaha (CST) a Zungeru, da Kwalejin Gudanarwa da Nazarin Kasuwanci (CABS) a Bida.[1]

Remove ads

Duba kuma

  • Jerin ilimin fasaha na poly a Najeriya

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads