Tauhidi
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Tauhidi: Itace kudurce Imani da kadaita Allah shi kadai, wato mutum ya yarda da Allah mahallici shi kadaine, kuma shi ya halicci kowa da komai. Kuma da imani da dukkanin Manzanni da Annabawan da Allah ya aiko su domin su karantar da mutane addini musulunci.
![]() |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
![]() |


Remove ads
Rabe-raben Tauhidi:
Tauhidi shine kadaita Allah SWT, a cikin abubuwa uku :
- [Tauhidur-rububiyya] wato kadaita Allah a cikin aiyukansa, shi kadai yayi halitta, shi kadai ya mallaki halitta, shi kadai yake gudanar da halitta, bashi da abokin tarayya, a cikin haka.
- Tauhidul-uluhiyya wato babu wanda ya cancanci bauta bisa gaskiya, sai Allah shi kadai.
- Duk Tauhidul-Asmaa'i wassafati, wato kadaita Allah taala, a cikin sunayan sa, da siffofinsa, wadanda sukazo a cikin Alkurani Mai girma da hadisai ingantattu.
Yarda da Gamsuwa Da Amincewa cewa Dukkan Labaran da Allah ya bayar, Ko Annabi S.A.W ya bayar, gaskiya ne, babu ja ko inke, haka dukkan hukuncin da Allah ya yanke, a Alkurani Mai girma, ko hadisai ingattatu, adalci ne.
Remove ads
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads