Tuwon shinkafa
Tuwon shinkafa abincine na mutanen Arewacin Najeriya. Shi wannan tuwon shinkafar ana yin shi ne da farar shinkafa wacce ba a tirara ta ba kafin a casa ta.An fi cinsa ne da miyar Taushe, duk da cewa ana cinsa da miyar kuka, kubewa, da sauransu. From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Tuwon shinkafa tuwon shinkafa dai yana cikin kalar abincin mutanen Arewacin Najeriya wato Hausawa.[1] Yana daga cikin nau'ikan tuwo. Sai dai shi ana yin sa ne da shinkafa. Ana haɗa shi da miyar kuka ko miyar taushe ko miyar kubewa wajen ci.[2]. Wato tuwon shinkafa yana daya daga cikin abincin gargajiya, saboda shi ma akan hada shi da garin masara wani sa’in. Amma mafi akasari wasu ba sa sa wa, sannan sunan tuwon shinkafa ya samo asali ne daga shinkafar da ake yinsa da ita. Kuma duk Najeriya ko a ina suna amfani da ita. Akan ci shi da kowace irin miya, amma an fi cin shi da miyar taushe.[3][4][5]



Remove ads
kayan Hadi
Shinkafar Tuwo
Ruwa[6]
Yadda ake hadawa
zaa wanke shinkafar
a zuba ruwa a tukunya idan ya tafasa sai a zuba shinkafar
idan shinkafar ta dahu sosai sai a dauko muciya aci gaba da tukawa har sai ta koma tuwo
sannan sai a rufe ta dan kara silala[7]
sai a kwashe
ana ci da miyan kubewa, tabshe, ogbono da sauran su
Bibiliyo
- Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
- Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads