Waliyi Abdurrahim-Maiduniya

From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Waliyi Abdurrahim-Maiduniya, wanda ake kiransa wani lokachin da Sheikh Abdurrahim ibn Ibrahim ibn Shi'ithu ibn Ghali, daga masarautar Kano yake kuma malamin addinin musulunci ne da yayi rayuwa a kasar Kadawa, ta Karamar Hukumar Warawa ta jihar Kano.[1]

Rayuwa

Waliyi Abdurrahim-Maiduniya ya kuma fito daga dangin Awliya Banu Gha Madinawa Malamai, zuriar Imam Ghali (Malam Gha),[2][3][4][5][6][7][8][9]wasu daga cikin dangin sa sunyi ikirarin asalinsu sun kasance daga Banu Hashim ne, Gidan Quraishawa wanda Larabawa ne, ta kuma wajen Sharif ibn Ali wanda ahalinsa suke mulkin kasar Morroco kuma wanda suke dangin Annabi Muhammadu ne,[10]ana kiran dangin nasa da sunan Madinawa saboda tarihin da ya nuna daga Madina suke,[11].[12][13][14]

Ya auri mata da dama a ciki har da Maryam Muhammad Inuwa Chango bafulatana daga garin Chango a Karamar hukumar Warawa ta dangin mahaifinta,[15]kuma yar Jobawa Fulani ta hanyar mahaifiyarta.[16]mahaifiyarta Binta yar Sarkin Sumaila Akilu ce wanda ya fito daga tsatson Makaman Kano Iliyasu da Makaman Kano Isa na Daya,[17]wanda suka rike sarautar Hakimichi a kasar Wudil, Garko, Takai da Sumaila Local Governments)[18]

Shi ne Kakan Abdullahi Aliyu Sumaila na wajen uba.[19]

Remove ads

Karamomi

Waliyi Abdurrahim Maiduniya ya kasance Limamin Kasar Kadawa ta Karamar Hukumar Warawa wanda aka itifakin Waliyi ne saboda Karamonin da yayi a zamanin rayuwarsa[20][21]

Tarihi ya nuna yayi zuhudu har wani lokachin ya na yin kwanaki bai ci abinci ba.[22]A masarautar Kano jama'a suna yin zaton Waliyi ne, Kabarinsa yana Kadawa.[23][24][25]

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads