Yankin Diffa

From Wikipedia, the free encyclopedia

Yankin Diffa
Remove ads

Yankin Diffa takasance ɗaya daga cikin yankunan gwamnatin ƙasar Nijar; babban birnin yankin itace Diffa.

Quick facts Wuri, Babban birni ...
Thumb
Diffa
Thumb
Taswirar Nijar: na nuna yankin Diffa a cikin launin Ja

Yankin Diffa yana bangaren kudu maso gabashin Nijar, kuma yana da girman murabba'in kilo mita 156,906.

Diffa na iyaka da yankin Agadez ta Arewaci da Zindar ta Yammaci da Najeriya ta kudanci sai kuma Chadi ta Gabashi.

Yankin Diffa ya kasance daya daga cikin yankunan da ba su da yawan jama'a, wanda kidayar shekara ta 2001, ta nuna yawan mutanen yankin ya kusa dubu dari hudu.

Jama'ar yankin Diffa sun hada da Kanuri da Tubawa Hausawa da Fulani da Larabawa.

Tattalin arzikin yankin Diffa ya ta'allaka ne kan kiwo da noman rani da kuma na damina.

Abubuwan da aka fi nomawa a yankin sun hada da gero da masara da shinkafa da kayan lambu irin timatir da barkono.

Sai dai kuma duk da noman da ake yi a Diffa, yankin ya kasance mafi koma baya ta fuskar noma a Nijar saboda fari.

Thumb
Landscape Diffa region Niger
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Thumb
kofar shiga cikin diffa
Remove ads
Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads