Nijar (ƙasa)
Ƙasa a yammacin Afirka From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Nijar ko Nijer[1][2] ƙasa ce da ke yankin Afrika ta Yamma. Tana maƙwabtaka da ƙasashe bakwai (Najeriya daga kudu, Libya daga arewa maso gabas, Aljeriya daga arewa maso yamma, Mali daga yamma, Burkina faso da Benin daga kudu maso yamma, Chadi daga gabas). Tana da al'umma da ta kai fiye da mutum miliyan sha bakwai (17) Kuma tana da ƙabilu daban-daban, kamar su: Hausawa, Zabarmawa, Abzinawa, Fulani, Kanuri, Bugaje, Barebari, Larabawa, Tubawa, da Gurmawa. Nijar ta na ɗaya daga cikin ƙasashen ƙungiyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Africa. (CEDEAO). Nijar tana da faɗin ƙasa kimanin 1,270,000Km (490,000sq mi) eta ta biyu 2 a fadin ƙasa, a ƙasashen Afirka ta yamma. Wajan 80% na ƙasar saharah ne, wajan 22 million mutanan ƙasar Nijar musulmai ne




Nijar ta samu 'yancin kanta a shekara ta 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Faransa. Tana da arziƙin ma'adanai na cikin ƙasa kamar zinariya, da ƙarfe, da gawayi, da uranium, da kuma fetur.
Remove ads
Al'umman Nijar 2013
A lissafin kasafin ƙasa da INS ta fitar [3], a shekara ta 2013 ƙasar Nijar tana da al'umma milyan sha bakwai da dubu ɗari da ashirin da tara da saba'in da shida (17,129,076).
Manyan Birane



Yankunan Gwamnatin kasar Sune kamar haka:
- Yankin Agadez
- Yankin Diffa
- Yankin Dosso
- Yankin Maradi
- Yankin Tahoua
- Yankin Tillabéri
- Yankin Zinder
- Niamey (Babban birni)
Birane da ke da adadin al'umma samada dubu goma (10,000) akan kidayar shekara ta 2012.
Remove ads
Hotuna
- Tutar kasar
- Matasa yan ƙabilar Wodaabe a kasar
- Akwai Sahara a kasar sosai
- Coat of Arms
- Nijar
- Taswirar kasar
- Kogin bank, Nijar
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |
MAnazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads