From Wikipedia, the free encyclopedia
Rita Auma Obama (an haife ta ne acikin shekara ta 1960) 'yar fafutukar ‘yancin jama’a ce ta Kenya da Burtaniya, masaniyar zamantakewa, ‘yar jarida, marubuciya, kuma 'yar'uwar shugaban Amurka na 44, Barack Obama . Obama tayi aiki a matsayin Shugabar zartarwa ta Gidauniyar Sauti (Gidauniyar Muryoyi masu Karfi), kungiya mai zaman kanta da ke taimaka wa marayu da sauran matasa da ke fama da talauci a Kenya. [1] [2]
Auma Obama | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nairobi, 1960 (63/64 shekaru) |
ƙasa | Kenya |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Barack Obama Sr. |
Mahaifiya | Kezia Obama |
Ahali | Barack Obama, Malik Obama (en) , Mark Okoth Obama Ndesandjo (en) , David Ndesandjo (en) , Abo Obama (en) , Bernard Obama (en) da George Hussein Onyango Obama (en) |
Karatu | |
Makaranta |
Heidelberg University (en) University of Bayreuth (en) Saarland University (en) |
Harsuna |
Turanci Jamusanci |
Sana'a | |
Sana'a | marubin wasannin kwaykwayo, marubuci da ɗan jarida |
Kyaututtuka |
gani
|
IMDb | nm3264073 |
Auma Obama 'diya ce ga Barack Obama Sr. da matarsa ta farko, Kezia Obama (née Aoko).[3][4][5] Ita ce 'yar uwar Barack Obama. Bayan ta halarci makarantar firamare ta gida da Makarantar Sakandare ta Kenya acikin shekara ta(1973)zuwa cikin shekara ta (1978), ta sami tallafin karatu don halartar jami'a a Jamus. Ta yi karanci Jamusanci a Jami'ar Heidelberg a cikin shekara ta 1981 har zuwa cikin shekara ta 1987. Bayan kammala karatunta daga Heidelberg, ta tafi karatun digiri a Jami'ar Bayreuth, ta kammala karatu da digiri na digirgir a Falsafanci a shekarar 1996. Ta kuma yi karatu a Kwalejin Fim da Talabijin ta Jamus a Berlin.[6] Ayyukan karshe na Obama a Kwalejin Fim shine fim na minti ashirin All That Glitters acikin shekara ta (1993), wanda ta haɗu da tarurruka na jinsi wajen nuna rashin lafiyar rayuwar baƙar fata a bayan hadin kan Jamus.[7]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.