From Wikipedia, the free encyclopedia
Charles Lindsay Temple (20 Nuwamba 1871 - 9 Janairu 1929) ya kasance Laftanar-Gwamnan Arewacin Najeriya daga Janairu 1914 har zuwa lokacin da rashin lafiya ya sa ya yi murabus daga muƙamin a shekara ta 1917.[1]
Charles Lindsay Temple | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1871 |
ƙasa | United Kingdom of Great Britain and Ireland |
Mutuwa | 1929 |
Yanayin mutuwa | (kidney failure (en) ) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Sir Richard Temple, 1st Baronet |
Mahaifiya | Mary Augusta Lindsay |
Abokiyar zama | Olive Temple (en) (28 ga Afirilu, 1912 - |
Karatu | |
Makaranta |
Sedbergh School (en) Trinity College (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a |
Temple shine ɗa ɗaya tilo daga auren na biyu na Sir Richard Temple, 1st Baronet, wanda ya auri Mary Augusta Lindsay a cikin Janairu 1871. An haife shi a Shimla, Indiya, a ranar 20 ga Nuwamba 1871. Ya yi karatu a Makarantar Sedbergh sannan ya shigar da shi Kwalejin Trinity, Cambridge a watan Yuni 1890, amma ya bar bayan ɗan lokaci kaɗan saboda rashin lafiya.[2]
Daga shekarar 1898 ya kasance mai riƙon mukamin jakadanci a Jihar Pará, Brazil, kuma daga 1899 zuwa 1901 mataimakin ƙaramin jakada a Manaus a wannan kasa. Bayan an mayar da shi Arewacin Najeriya a 1901, sai aka naɗa shi CMG don hidimar diflomasiyya a 1909[3] and rose to become Lieutenant-Governor of that region in 1914.[2][4] kuma ya zama Laftanar-Gwamnan yankin a 1914.
Ya auri Olive MacLeod, 'yar Sir Reginald MacLeod na MacLeod, a cikin 1912.[5] Ya mutu a Granada, Sifaniya, a dalilin ciwon ƙoda a ranar 9 ga Janairu 1929.[1]
A shekarar 1915, Olive da Charles sun buga littafi kan rayuwarsu a Najeriya mai suna Notes on the Tribes, Provinces, Emirates and States of Northern Provinces of Nigeria.[6][7]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.