Gombe (jiha)
jiha a Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Gombe jiha ce dake Arewa maso Gabashin Najeriya. Tayi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Borno da Yobe, daga Kudu kuwa da Jihar Taraba, daga Kudu maso yamma kuwa da Jihar Adamawa sannan daga Yamma da Jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta daga babban birninta kuma yanki mafi girma a jihar wato Babban Birnin Gombe - kuma an ƙirƙireta ne daga sashin Jihar Bauchi a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta alif ɗari tara da cassain da shida 1996. Jihar na daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙabilu iri-iri a Najeriya. Acikin jihohi 36 da Abuja na Najeriya, Jihar Gombe itace Jiha ta 21 a girma, kuma ta 32 a yawan jama'a, da mutane aƙalla miliyan 3.25 dangane da ƙiyasin shekara ta 2016.[1]
Gombe | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Suna saboda | Gombe | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Gombe | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,256,962 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 173.54 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 18,768 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Bauchi | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Gombe State (en) | ||||
Gangar majalisa | Gombe State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-GO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | mof.gm.gov.ng |
Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar tana da ƙasa nau'in Tropical West Sudanian Savanna. Muhimman wurare a jihar sun haɗa Kogin Gongola, wanda ke kwarara ta arewaci da Gabashin Gombe zuwa cikin tafkin Dadin Kowa Dam zuwa gaɓar Tsaunukan Muri da ke can yankin kudancin jihar. Daga cikin dabbobi asali na jihar akwai nau'in macizai irin su: carpet viper, puff adder, da kuma Egyptian cobra da kuma dabbobi irin su dorinar ruwa, Senegal parrot, da kuma grey-headed kingfisher.
Jihar Gombe na ɗauke da ƙabilu da dama, yayinda Ƙabilar Fulani suka mamaye yankin arewaci da tsakiyar jihar tare da Bolewa, Kanuri, da kuma Hausawa. A yayin ƙabilu irin su Cham, Dadiya, Jaranci da Kamo, Pero, Tangale, Tera, da kuma mutanen Waja da suka mamaye yankunan gabashi da kudancin jihar.
Kafin zuwan Turawa, yankin Jihar Gombe ta yau tana ɗauke da ƙasashe da dama masu zaman kansu, har zuwa farkon karni na 1800, lokacin da Fulani suka ƙwace yankuna da dama na yankin kuma suka haɗeta a matsayin Masarautar Gombe a ƙarƙashin Daular Sokoto. A cikin karni na 1900, Turawan mulkin mallaka sun mamaye masarautar da yankunan gefen ta kuma sun haɗeta acikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya, inda daga baya ta zamo Colonial Nigeria, kafin daga bisani ta samu 'yanci a1960 kuma ta zamo ƙasa Najeriya. Bayan samun 'yancin kai kuwa, Jihar Gombe ta yau ta faɗa ƙarƙashin Arewacin Najeriya har zuwa 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta faɗa ƙarƙashin Jihar Arewa ta Gabas. Bayan an raba Jihar Arewa maso Gabas, an ƙirƙiri Jihar Bauchi a shekarar 1976 tare da Sauran jihohi guda goma. Shekaru ashirin bayan haka (1996) an cire wasu gungun ƙananan hukumomi daga yammacin Jihar Bauchi don samar da Jihar Gombe.
Dangane da fannin tattalin arziƙi, Jihar Gombe ta dogara ne akan noma da kiwo, da man fetur, inda ake shuka gero, masara, gyaɗa, dawa da tumatir tare da kiwon dabbobi kamarsu raƙumma, shanu, akuyoyi da kuma tumaki. Sauran muhimman masana'antu sun haɗa da hidindimu na zamani da ake gudanarwa musamman a birnin Gombe. Jihar Gombe itace jiha ta huɗu a jerin ƙarancin Cigaban al'ummaa.
Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 18,768 da yawan jama’a miliyan biyu da dubu uku da hamsin da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gombe. Muhammadx Inuwa Yahaya shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Dr Manasa Daniel Jatau. Dattijan jihar su ne: Sarakunan gargajiya, Malaman addini da kuma jigogin siyasa.[2]