Adeline Akufo-Addo

From Wikipedia, the free encyclopedia

Remove ads

Adeline Sylvia Eugenia Ama Yeboakua Akufo-Addo (née Nana Yeboakua Ofori-Atta; 17 ga watan Disamban a shekara ta 1917 - 21 Maris din shekarar 2004) matar shugaban kasa ce a jamhuriya ta biyu ta Ghana a matsayin matar Edward Akufo-Addo kuma mahaifiyar shugaban Ghana Nana Akufo- Addo .

Quick facts Rayuwa, Haihuwa ...

Ta mutu a asibitin koyarwa na Korle-Bu da ke Accra a ranar 21 ga watan Maris na shekara ta 2004, tana da shekara 86.[1]

Remove ads

Rayuwa ta sirri

An haife tane ga Nana Sir Ofori Atta I, Omanhene na Akyem Abuakwa, da Agnes Akosua Dodua na Abomosu,[1] ita ce kuma Abontendomhene (sarauniyar gidan sarauta na Ofori Panin Fie na Kyebi). Don haka, an sanya mata salo a hukumance a matsayin Nana Yeboakua Ofori-Atta.[2][3]

Yayarta ita ce Susan Ofori-Atta, likita mace ta farko daga Gold Coast.[4][5][6][7] Babban ɗan'uwan Adeline Akufo-Addo shine William Ofori-Atta, ɗan siyasan Gold Coast kuma lauya, tsohon ministan harkokin waje kuma ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa United Gold Coast Convention (UGCC) da kuma memba na "Manyan shida", Kungiyar masu fafutuka ta siyasa da gwamnatin mulkin mallaka ta Burtaniya ta tsare bayan tarzomar Accra a shekara ta 1948, inda suka fara fafutukar ganin Ghana ta sami 'yancin kai a shekarar 1957. Wani dan uwanta shi ne Kofi Asante Ofori-Atta, ministan kananan hukumomi a jam'iyyar Convention People's Party (CPP) ta gwamnatin Kwame Nkrumah kuma daga bisani shugaban majalisar dokokin Ghana.[8]

Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads