Bala Mohammed
Ɗan siyasar Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Bala Mohammed (Inkiya Kauran Bauchi) An haife shi ne a farkon Watan Oktoban shekarar ta alif dari tara da hamsin da takwas, 1958)[1] Miladiyya.(A.c) Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982, Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a shekarar 1983 Bio[permanent dead link] bayan ya kammala karatu. Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000, Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka haɗa da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A ƙarshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a Nigerian Meteorological Agency. Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a shekarar 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin Yar'adua. Labarai LABARAI Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado Talata, Maris 26, 2019 at 7:04 Safiya by Muhammad Malumfashi A jiya ne hukumar zaɓe na INEC ta sanar da cewa Sanata Bala Mohammed ne ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a jihar Bauchi inda ya doke gwamna mai-ci. Mun kawo kaɗan daga tarihin Kauran Bauchi News.
Remove ads
Tarihi
- Haihuwa da karatu An haifi Bala Abdulkadir Mohammed ne a farkon Watan Oktoban 1958, kenan yana da shekaru 60 yanzu a Duniya. Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982.
- Aikace-aikace Sanata Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a 1983 bayan ya kammala karatu. Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000.
- Aikin Gwamnati Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka haɗa da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A ƙarshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a (Nigerian Meteorological Agency). Sabon gwamnan ya kuma yi aiki a hukumar da ke kula da jirgin kasa a Najeriya watau (Nigerian Railway Corporation) daga shekara ta 2005 har 2007. Kafin nan kuma yayi aiki da Isa Yuguda a matsayin mai ba sa shawara daga 2000 zuwa 2005.
- Siyasar Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin 'Yaradua. A shekarar 2010 ne shugaban kasa na rikon kwarya watau Goodluck Jonathan ya nada Bala Mohammed a matsayin Ministan babban birnin tarayya Abuja har zuwa 2015. Sanatan yana cikin waɗanda suka fara cewa a naɗa Jonathan kan mulki a wancan lokaci. A zaɓen 2019 ne Bala Mohammed ya doke gwamna Mohammed Abubakar, na jam’iyyar APC inda ya samu kuri’u 515,113. APC ta samu kuri’a 500,625 ne a zaɓen inji hukumar INEC mai zaman kan-ta.
Remove ads
Manazarta
Education and career
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads