Bulgeriya[1] ko Bulgaria ƙasa ce, da ke a nahiyar Turai. Babban birnin ƙasar Bulgariya Sofiya ne. Bulgeriya tana da yawan fili kimani na kilomita araba'i 110,993. Bulgeriya tana da yawan jama'a 7,000,039, bisa ga jimilla a shekarar 2019. Bulgeriya tana da iyaka da ƙasashen biyar: Romainiya a Arewa, Serbiya da Masadoiniya ta Arewa a Yamma, Girka da Turkiyya a Kudu.Bulgeriya ta samu yancin kanta a shekara ta 1878 (akwai ƙasar Bulgeriya mai mulkin kai daga karni na bakwai bayan haihuwar Annabi Isah zuwa karni na sha ɗaya, da daga karni na sha biyu zuwa karni na sha huɗu).