CNN

From Wikipedia, the free encyclopedia

CNN
Remove ads

CNN,(Cable News Network) tashar watsa labarai ce ta ƙasa da ƙasa mai hedikwata a Atlanta, Jojiya, Amurka.[1][2][3] An kafa ta a cikin shekarata 1980 ta hannun mai mallakar kafofin watsa labarai na Amurka Ted Turner da Reese Schonfeld a matsayin tashar watsa labarai na tsawon sa'o'i 24 a kullum, kuma a halin yanzu mallakar kamfanin na watsa labarai na hannun Manhattan, Warner Bros. Discovery.[4] CNN ita ce tashar talabijin ta farko da ta fara watsa labarai tsawon sa'o'i 24. Kuma tashar talabijin ta farko- da ta fara watsa labarai a Amurka.[5][6][7][8][9]

Quick Facts URL (en), Iri ...
Thumb
gidan telebijin ccn da ke kasar amurka
Thumb
gaban gidan telebijin CCN


Tun daga watan Satumba na shekarar 2018, CNN tana da masu mu'amala (subscribers) da tashar mutane miliyan 90.1 a matsayin masu biyan kuɗi (subscriptions), kuma (kashi 97.7% cikin 100 na masu mu'amala da tashar, na da tashar acikin akwatunan telebijin nasu a gidajen su).[10] MSNBC, matsakaicin masu kallo 580,000 a ko'ina cikin yini, ya ragu da kashi 49% daga shekarar da ta gabata, a cikin raguwar masu kallo a duka hanyoyin sadarwar tashar (channels).[11] Yayin da CNN ke a matsayi na 14 a cikin jerin tashoshin watsa labarai a shekara ta 2019,[12][13] gidan telebijin ɗin yayi kukan kura inda ya zabura izuwa mataki na 7th daga mataki na 14 da yake abaya. Acikin manyan hanyoyin sadarwa da sukayi fice akwai; (Fox News a mataki na 5, da MSNBC a mataki na 6, a wannan shekarar),[14] ta koma mataki na 11 a shekarar 2021.[15]

A duk duniya, shirye-shiryen CNN ana watsawa ta hanyar CNN International, waɗanda masu kallo ke gani a cikin ƙasashe da yankuna sama da 212;[16] tun daga watan Mayu 2019. Gidan talabijin ɗin mallakar Amurka, ana takaita sunan da CNN (US), Bugu da ƙari tana watsa shirye-shiryen ta a Kanada, wasu tsibiran Caribbean da kuma a Japan, inda aka fara watsa shirye-shirye a kafar yaɗa labarai ta CNNj a shekara ta 2003, tare da fassarar lokaci guda cikin harshen Jafananci.[17]

Remove ads

Tarihi

Kana iya karanta cikakken tarihin CNN anan

See also: History of CNN

An kaddamar da Cable News Network da karfe 5:00 na yamma, a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 1980. Bayan gabatarwa daga; Ted Turner, David Walker da matarsa Lois Hart sune na farko da suka fara jawabi/watsa shiri a tashar.[18] Burt Reinhardt, mataimakin shugaban zartaswa na CNN, ya ɗauki mafi yawan ma'aikatan tashar su 200 na farko, ciki aka watsa shiri na faro da aka ma shirin laƙabi da, news anchor wanda, ɗan jarida Bernard Shaw ne, ya gabatar da shirin.[19]

Tun farkon farawa, CNN ta faɗaɗa hanyar isar da shirye-shiryen ta izuwa sassa daban-daban ta hanyar tauraron ɗan adam, gidajen yanar gizo, da tashoshi na musamman na (kamar CNN Airport). Kamfanin yana da ofisoshi 42 (11 na cikin gida, 31 na ƙasashen waje),[20] fiye da tashoshin gida na haɗin gwiwar 900 (wanda kuma ke karɓar labarai da abubuwan da ke ciki ta hanyar sabis na labarai na bidiyo na CNN Newsource),[21] da kuma cibiyoyin sadarwa na yanki da na waje da dama a duniya.[22] Nasarar tashar ya dogara kacokan akan babban wanda ya kafa ta Ted Turner, kamfanin Time Warner ada ana kiranta da WarnerMedia sai yayi maja da Discovery Inc. aka samar da Warner Bros. Discovery) Wanda a ƙarshe y mallaki kafofin Watsa Labarai na rukunin Turner Broadcasting System a shekarar 1996.[23][24]

Remove ads

Shirye-shirye

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads