Chevron
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Kamfanin Chevron (NYSE) kamfanin mai ne babba na ƙasashen duniya, tushen sa na can Ramon, California.[1] An samar da kamfanin a shekarar 1984[2] kuma shi ne na uku a jerin manyan kamfononin man-fetur a Amurka. Yana ɗaukar sama da mutane dubu sitin 60,000 aiki. Yana ɗaya daga cikin manyan kamfanonin matatar mai guda shida a duniya.



Daga cikin harkokin kamfanin Chevron akwai hade-hade da sayar da hajojin man-fetur, maya-mayan inji, da sauran sinadarai da ake iya samu daga fetur. Wuraren da kamfanin tafi gudanar da harkokinta sun hada da yammacin gabar tekun Arewacin Amurka, Gulf Coast dake Amurka, Kudu-maso yammacin Asiya, Korea ta Kudu, da kasar Australia. A shekara ta 2018, kamfanin tana samar da akasarin barrel 791,000 a duk rana.[3]
Remove ads
Tarihi
An kirkiri kamfanin Chevron a shekaran 1987, amma tarihin kamfanin ya fara tun watan Satumba na shekara 1879, lokacinda tsohon kamfanin na asali wato "Star Oil"[4] ta soma hako mai a Filin-mai na Pico Canyon dake tsibirin Santo Susana dake arewacin Los Angeles a shekarar 1876, an ƙirƙiro Kamfanin Mai na Pacific Coast. Sun riƙe sunan har zuwa shekara ta 1906, lokacin da ta haɗu da wani kamfanin mai suna Standard Oil kuma ya zama Kamfanin Mai na (California).[2] Standard Oil na California da Gulf Oil sun haɗu a cikin shekara ta 1984, wanda ya zama babbar haɗuwa a tarihi a wancan lokacin. Kamfanin zai canza sunansa zuwa Chevron Corporation a shekarar.[5]
A watan Satumban shekarata 1879 Charles N Felton da Lloyd Tevis da George Looms da sauransu suka kirkiri Kamfanin "Pacific Oil Coast Company", wanda daga baya ta mamaye hannun jarrin " Star Oil"[6] da jarin kudi dalala $1million.[7]Man Kamfanin Pacific ya zamo mafi soyuwa a garin California[8] daga baya kuma kamfanin "Standard Oil" ta siye ta akan kudi dala $761000 a 1900.[4]Kamfanin Pacific ta ci gaba da gudanar da harkokinta na yau da kullum da sunanta har zuwa shekarar 1906, lokacin da aka hade ta da wani karamin kamfanin Standard Oil sai ya koma Standard Oil California ko California Standard.[9][10]
Sai kuma mabiyinsa wato Texas Fuel Company wanda aka samat, a. Shekarar 1901 a garin. Beaumont dake Texas a matsayin dillalin kayan man-fetur wanda Bucksin ya samr. Kamfanin Texas Fuel sunyi aiki kusa da kusa da kamfanin Chevron. A shekarar 1936, kamfaninTexas sunyi hadin gwiwa da kamfanin Standard California don gina rijiyan mai a Saudiyya, wanda aka sanya wa inkiya da "Caltex".[11]Texas Fuel Company ya koma Texas Company daga baya kuma Texaco.[12][13]
A shekara ta 2000, kamfanin Chevron ta siya Texaco akan harkallan kudi dala Biliyan $45, wanda ya maida kamfanin na biyu a girma a duk fadin Amurka kuma na hudu a jerin manyan kamfanonin hada-hadan man fetur na duniya.[2]
Remove ads
Jagoranchi
Micheal Wirth shi ne chairman kuma CEO na Kamfanin Chevron na yanzu[14]
Sauran yanar gizo
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads