Edo

Jiha ce a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia

Edo
Remove ads

Jihar Edo Jiha ce dake kudu maso kudancin Najeriya.[1] Babban birnin jihar shi ne Benin. Dangane da ƙidayar shekara ta 2006, Jihar ita ce ta shida a yawan jama'a da adadin mutane kimanin 3,233,366.[2] Edo ita ce ta 22 a faɗin ƙasa a Najeriya.[3] Babban birnin jihar shi ne Benin City, ita ce birni ta hudu a girma a Najeriya, kuma ta ƙunshi cibiyar masana'antun roba a Najeriya.[4][5] An ƙirƙire ta a shekarar 1991, daga tsohuwar Jihar Bendel, kuma ana kiranta da kuma suna "Heart beat of the Nation" (bugun zuciyan ƙasa).[6]

Thumb
Manyan makarantun jihar edo
Quick Facts Wuri, Babban birni ...
Thumb
Lambar motar jihar edo
Thumb
Masallacin unguwar auchi dake birnin Edo
Thumb
Gidan talabijin na jihar Edo
Thumb
jami'ar Edo
Thumb

Jihar Edo tana da iyaka da Jihar Kogi daga arewa maso gabas, Jihar Anambra da ga gabas, Jihar Delta daga kudu maso gabas da kudu maso kudancin jihar, Jihar Ondo kuma daga yamma.[7]

Yankunan Jihar Edo a yau sun haɗa iyaka da masarautun da dauloli da aka kafa tun a ƙarni na 11 miladiyya, harda Masarautar Benin.[8] A shekarar alif 1897, Daular Burtaniya ta ƙaddamar da wata azzalimar ziyara ga yankin Benin, inda suka tarwatsa tsaffin biranen Edo, inda suka haɗe su a cikin yankin da ta zamo Yankin mulkin mallaka na Kudancin Najeriya.[9][10]

Edo jiha ce dake ɗauke da mutane iri-iri musamman Harsunan Edoid da kuma Mutanen Edo ko Bini,[11] Esan, Kabilar Owan, Afemai.[12] Harshen da yafi fice daga cikin yarukan Edo shine Yaren Edo wanda akae yawan amfani dashi a Birnin Benin.[13] Mafi yawa mutanen Jihar mabiya addinin Kiristanci ne. Turawan mishanari na Portugal suka kawo addinin a yankin a ƙarni na 15. Akwai 'yan tsirarun mabiya addinin Musulunci da addinan gargajiya.[14]

Remove ads

Tarihi

Yankin Yamma ta Tsakiya, Najeriya yanki ne a Najeriya a tsakanin shekarun 1963 zuwa 1991. Kuma ana kiranta da Jihar Bendel daga shekarar 1976. An ƙirƙiri jihar a watan June 1963, daga yankin gundumomin Benin da Delta na Yankin Yammacin Najeriya, kuma babban birninta shi ne Benin City.[15] An canza mata suna zuwa gunduma a 1966, sannna kuma a 1967 lokacin da aka rarraba sauran gundumomin zuwa jihohi da dama, ta tsaya a matsayin yanki, kafin daga bisani ta zamo jiha.[16]

A lokacin Yaƙin basasar Najeriya, sojojin Biyafara sun kai wa sabuwar jihar Yankin Yamma ta Tsakiya hari, wacce ta haɗa hanya da Lagos, a wata yunkuri na tilasta kawo karshen yakin. A yayin wannan fafatawar, an sanya wa jihar suna ''Jamhuriyar Benin gabanin sojojin Najeriya su sake ƙwato yankin. Jimhuriyar ta zo ƙarshe na tsawon yini ɗaya bayan sojojin Najeriya sun kwace birnin Benin City. An ƙirƙiri jihar Edo a ranar 27 ga watan Augustan 1991, a lokacin da aka raba Jihar Bendel zuwa jihohin Edo da Delta.[17][18]

Remove ads

Mutane

Thumb
Mutanen Edo

Tare da Birnin Benin a matsayin babban birnin jihar, yawan mutanen garin sun kai kimanin mutum miliyan 8.[19] Jihar ta kunshi muhimman kabilu guda hudu sune: Kabilar Edo (mutanen Bini, Owan, Esan, Afemai (Etsakọ da kuma Akoko-Edo). A jihar akwai mutane daga yankuna da dama daga sassa daban daban na duniya. Birnin bini yana da tarihin zama daya daga cikin yankunan da Turawa suka zauna a zamanin ziyarar su Nahiyar Afirka daruruwan shekaru da suka gabata. Wasu daga cikin wadannan yankuna sun zamo wuraren ziyaran buda idanu a yau.[20]

Remove ads

Zamantakewa

Thumb
Edo

Muhimman kabilun Jihar Edo sun hada da kabilun Bini, Etsako, Esan, Owan da kuma kabilar Akoko Edo.[19] Yawancin wadannan Kabilu sun samo asalli ne daga babban birnin Benin City, a dalilin haka harsunansu sun bambanta ne dangane da nisansu da babban birnin. Kabilar Bini sun mamaye kananan hukumomi guda bakwai daga cikin kananan hukumomi 18 dake jihar kuma sun kwashe kaso 57.54% na yawan mutanen Jihar. Sauran kuma: Esan (17.14%), Etsako (12.19%), Owan (7.43%), da kuma Akoko Edo (5.70%).[19] Amma kuma akwai yarukan dake zaune a yankunan Akoko Edo, su kuma Itsekiri na zaune a yankin Ikpoba-Okha, da kuma harsunan IjawIzons, Urhobos dake zaune a kananan hukumomin Ovia ta Arewa maso Gabas da Kudu maso Yamma da kuma yankunan iyakokin jihar. Har wayau, ana samun mutanen Ibo a yanki Igbanke(Ika) dake karamar hukumar Orhionmwon.[21]

Gwamnoni

Ƙarin bayanai Suna, Take ...
Thumb
Ososo Hills
Remove ads

Kananan Hukumomi

Jihar Edo nada Kananan hukumomi guda goma sha takwas (18). Sune:

Yankunan Majalisar Dokokin Jihar Edo (Majalisa ta Biyar) a shekara ta 2013

Majalisar Dokokin Jihar Edo a shekara ta 2013 ta kunshi yankuna guda ashirin da hudu (24)

Remove ads

Sashen Shari'a na Jihar Edo

Sashen Shari'a itace mataki na uku na gwamnatin Jihar Edo, wacce ke da alhakin zartar da shari'a da kuma sasanta rigingimu na al'umma da kuma masu laifi a jihar. A ranar 16 ga watab Mayun 2021 ne, Gwamna Obaseki ya rantsar da Mai Shari'a Joe Acha a matsayin a matsayin Alkalin Alkalai na rikon kwarya a Jihar Edo, bayan mai shari'a Esther Edigin ya ajiye aiki.[25]

Siyasa

Godwin Obaseki ne gwamnan jihar Edo na yanzu kuma an rantsar da shi a ranar 12 ga watan Nuwamban, 2016.[26] Mataimakinshi kuma shine Comrade Philip Shaibu.[27]

Harsuna

Turanci ne harshen gwamnati a jihar. Yarukan da ake magana dasu a jihar sun hada da:Harshen Edo, Igarra, Etsako/Afemai, Harshen Esan da kuma Yaren Okpamheri.[28] Jihar Edo gida ne ga wasu harsunan kamar; Edo, Okpe, Okpe, Esan, Ora, Akoko-Edo, Igbanke, Emai.[29][30][31]

Kabilun Etsako/Afemai ne ke da mafiya yawan musulmai a jihar. Sun mamaye kananan hukumomi shida kuma muhimmin aikinsu shine noma.[32]

Harsunan Jihar Edo dangane da kananan hukumomin jihar.[33]

Ƙarin bayanai LGA, Languages ...

Addinai

Mafi yawan mutanen Jihar Edo mabiya addinin Kirista ne tare da tsiraru daga cikin mabiya addinin Musulunci da addinan gargajiya.[34][35]

Tattalin arziki

Wuraren ziyara na Jihar Edo sun hada da; Mutum-mutumin Emotan dake cikin Birnin Benin, koramar Ise, da wurin shakatawa na gabar Kogin Niger wato Agenebode. Etsako-East; Mike Akhigbe Square dake fugar, Ambrose Alli Square, Ekpoma, River Niger Beaches da ke Ilushi, BFFM Building dake Ewu, Igun Bronze Caster da ke Igun Street a birnin Benin City, Kwalejin numa da kiwon halittun ruwa (Agriculture and Aqua Culture Technology, Agenebode), Okpekpe da tsaunukan ta da wuraren kallo, tsaunin Usomege Hills, Apana-Uzairue, Somorika hills da ke Akoko Edo inda akwai wurin bude ido da gwamnati ta a shirya a Ososo da kyawawan wuraren kallon.[36][37]

Jihar tana samar da man fetur[38] da sauran ma'adanai kamar farar kasa da dutsen kwaru. Jihar tana da kamfanin siminti a Okpilla.[39] da kamfanin fulawa a Ewu wanda ke kawo karshe.[39]

Remove ads

Ma'adanai

Ma'adinan da ake iya samu a jihar sun hada da:[40]

  • Asphalt/Bitumen
  • Clay
  • Dolomite (mineral)/Dolomite
  • Phosphate
  • Glass/Glass-sand
  • Gold
  • Gypsum/Gypsium
  • Iron ore/Iron-ore
  • Lignite
  • Limestone
  • Marble
  • Fossil fuel/Oil/Gas

Ilimi

Makarantu na gaba da sakandare a Jihar Edo sun hada da:

Kiwon Lafiya

Jerin wuraren kiwon lafiya na Jihar Edo da kananan hukumomin da suke.[55]

Medical Zone Local Government Name Of Hospital Medical Zone Local Government Name Of Hospital Medical Zone Local Government Name Of Hospital
Abudu Orhionmwon General Hospital, Abudu[56] Benin Oredo Central Hospital B/City[57] Igarra Akoko Edo General Hospital, Igarra
Abudu Orhionmwon General Hospital, Igbanke[58] Benin Oredo Cottage. Hospital Obayantor[59][60] Igarra Akoko Edo Government Hospital, Ibillo
Abudu Orhionmwon General Hospital, Uronigbe[61] Benin Oredo Stella Obasanjo Hospital[62][63][60] Etete Layout Road, Benin City Dist. Hospital, Uneme-Osu
Abudu Orhionmwon Cot. Hospital Oben Ekpoma Esan West General Hospital, Ekpoma[64] Iguobazuwa Ovia South West General Hospital. Iguobazuwa
Abudu Orhionmwon Cot. Hospital Egbokor Ekpoma Esan West General Hospital, Iruekpen Iguobazuwa Ovia South West Government Hospital Usen
Abudu Uhunmwode Dist. Hospital, Egba Ekpoma Esan Central Dist. Hospital, Usugbenu Iguobazuwa Ovia North East Dist. Hospital, Ekiadolor
Afuze Owan East General Hospital, Afuze[65] Ekpoma Esan Central Dist. Hospital, Ewu Ossiomo Leprosy Clinic in All L.G.A Specislist Hospital, Ossiomo
Afuze Owan East Dist. Hospital, Otuo Fugar Etsako East General Hospital, Fugar Ubiaja Esan South West General Hospital, Ubiaja
Afuze Owan West General Hospital, Sabogida Ora[66] Fugar Etsako East General Hospital, Agenebode Ubiaja Esan South West Dist. Hospital, Ewohimi
Afuze Owan West Dist. Hospital, Uzebba Fugar Etsako East Dist. Hospital, Apana Ubiaja Igueben Government Hospital, Igueben
Auchi Estako West Central. Hospital, Auchi[67] Fugar Etsako West Government Hospital, Agbede Uromi Esan North East Central Hospital Uromi

Shahararrun Mutane

  • Oba of Benin[68]
  • John Odigie Oyegun, Gwamnan farko na Jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC[69][70]
  • Godwin Obaseki, Tsohon chiyaman na jiha na kungiyar harkokin tattalin arziki kuma Gwamnan Jihar Edo na yanzu[71][72]
  • Jeffrey Obomeghie, Babban jami'i na asibitin International Hospitality Institute da marubuci[73]
  • Erhabor Emokpae, wanda ya fara fasaha na zamani a Najeriya[74]
  • Admiral Mike Akhigbe, tsohon mataimakin shugaban kasa na Federal Republic of Nigeria.[75]
  • Dele Giwa, dan jarida a Najeriya, edita kuma wanda ya kirkiri mujallar Newswatch.[76][77]
  • Senator Albert Legogie, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa na Jamhuriya ta Uku kuma mafarin "Board of Trustees" na Peoples Democratic Party (PDP).[78]
  • Pa Michael Imoudu, shugaban labour kuma and founder of the Nigeria state,[79]
  • Chief Julius Momo Udochi, jakadan Najeriya na farko da kasar Amurka,[80]
  • Gen. George Agbazika Innih, gwamna na dan-lokaci a zamanin mulkin soji Bendel and Kwara State,[81]
  • Major-General Abdul Rahman Mamudu tsohon kwamanda Nigerian Army "Signals Corps and military administrator" Gongola State,[82]
  • Aigboje Aig-Imoukhuede, wanda ya taimaka wajen kirkirar bankin Access Bank Plc kuma ya kirkiri "Africa Initiative for Governance" (AIG)[83][84]
  • Adams Oshiomhole, tsohon shugaban Nigeria Labour Congress kuma tsohon gwamnan Jihar Edo; shi ya gina Edo University da ke Iyamoh, Jihar Edo.[85][86]
  • Pastor Chris Oyakhilome, wanda ya kirkiri Believers Loveworld Nation[87][88]
  • Prince Tony Momoh, tsohon ministan Labarai da al'adu (Information and Culture)[89][90]
  • Maymunah Kadiri, Wakilin masu tabun hankali a Najeriya[91][92]
  • Commander Anthony Ikhazoboh, ministan wasanni da zurga-zurga[Ana bukatan hujja]
  • Professor Ambrose Alli, tsohon gwamnan Jihar Bendel da ta shude. Shi ya kirkiri Jami'ar Jihar Bendel kuma an sanya mata sunanshi a yau.[93][94]
  • John Momoh, dan jarida mai watsa labari kuma CEO na Channels TV[95][96]
  • Professor Osayuki Godwin Oshodin, tsohon vice chancellor na University of Benin[97][98]
  • Jacob U. Egharevba, a Bini masanin tarihi kuma jagora na gargajiya[99]
  • Dr Samuel Ogbemudia, tsohon gwamnan Yankin Yamma ta Tsakiya na Najeriya kuma daga bisani na Jihar Bendel[100][101][102]
  • Chief Anthony Enahoro, dan adawa da mulkin mallaka kuma mai and pro-democracy activist and politician[103][104]
  • Professor Festus Iyayi, marubucin littattafai kuma dan Afurka na farko da ya fara lashe lamban yao na Commonwealth Writers Prize[105][106]
  • Odia Ofeimun, mahikyanci kuma tsohon shugaban Association of Nigerian Authors[107][108]
  • Dr Abel Guobadia, mai ilimantarwa kuma tsohon jakadan Najeriya da Republic of Korea, tsohon Chairman Independent National Electoral Commission (INEC)[109][110]
  • General Godwin Abbe, tsohon ministan Najeriya akan Tsaron cikin Gida[111][112]
  • Archbishop John Edokpolo, wanda ya kirkiri makarantar Edokpolo Grammar Schools and Political Activist[113][114]
  • Sir Victor Uwaifo, mawakai[115]
  • Archbishop Benson Idahosa, shugaban cocin Pentecost[116][117]
  • Sonny Okosun, mawaki[118][119]
  • Augustine Eguavoen, tsohon dan wasan kwallafa na kwararru na Najeriya pkuma mai horo [120]
  • Felix Idubor, artist[121]
  • Festus Ezeli, dan wasan kwallon kwando wanda yayi wasa a kungiyar Golden State Warriors[122]
  • Modupe Ozolua, likitan habaka jiki da surgery[123][124]
  • Chief Tony Anenih, chairman na kwamitin amintattu na (PDP) tsohon Ministan Ayyuka.[125][126]
  • Gabriel Igbinedion, international business mogul kuma babban chife na bini, me ITV[127][128]
  • Raymond Dokpesi, me babban gidan telebijin a Afurka kuma dan siyasa[129][130][131]
  • Lancelot Oduwa Imasuen, film director, screenwriter and producer[132]
  • Suyi Davies Okungbowa, marubuci kirkirarren labari da kuma labarai na almara[133][134]
  • Osaze Peter Odemwingie, kwararren dan wasan kwallon kafa[135][136]
  • Chris Aire-Iluobe, mai sana'ar jauhari kuma designer[137][138]
  • Francis Edo-Osagie, dan kasuwa [Ana bukatan hujja]
  • Kamaru Usman, kwararren dan damben mixed martial arts wanda aka baiwa kwantiragin Ultimate Fighting Championship, kuma welterweight champion.[139]
  • Yakubu Ayegbeni, tsohon kwararren dan wasan kwallon kafa[140][141][142]
  • Rema (Nigerian musician), mawaki wanda ya sa hannu da Mavin Records,[143]
  • Philip Shaibu (haihuwar 1 December 1969, a Kaduna) tsohon dalbi a University of Jos alkali ne a Najeriya, dan siyasa kuma dan kasuwa. Shine mataimakin gwamnan Jihar Edo na yanzu .[144]
  • Eghosa Asemota Agbonifo, politician, coordinator of Michael Agbonifo shoe a child foundation[145]
  • Prof T. M. Yesufu, wanda ya fara zama Vice-Chancellor a Jami'ar Benin, economist.[146][147]
  • Odion Jude Ighalo, kwararren dan wasan kwallon kafa.[148]
  • Victor Osimhen, kwararren dan wasan kwallon kafa.[149][150]
  • Aisha Yesufu, 'Yar gwarmayar siyasa akan zamantakewa a Najeriya.[151][152]
  • Yvonne Jegede jaruman, furodusan fina-finai, 'yar talla, kuma mai fitowa a shiri Telebijin; musamman wajen shirya 3 is Company.[153]
  • Zakariyau Oseni, shaharrren farfesa na Larabci kuma malami a Islamic studies, guardian of Arabic language da literature, kuma limami kuma poet.[154]
  • Mike Ozekhome, mai kare hakki da 'yan dan Adam.[155]
  • Mike Oghiadomhe, chief of staff na shugaban kasa Goodluck Jonathan in 2014.[156][157]
  • Solomon Arase, tsohon kuma Inspeta jenar na 'Yan sanda a Najeriya karkashin shugaba mulkin Goodluck Jonathan.[158][159]
  • Julius Aghahowa, kwararren dan wasan kwallon kafa.[160][161]
  • Sam Loco Efe (1945-2011), tsohon jarumin Nollywood kuma furodusa.[162][163]
  • Admiral Augustus Aikhomu,tsohon chief of staff a lokacin General Ibrahim Babangida administration.[164]
  • Helen Paul, 'yar barkwanci kuma jaruma kuma an santa da Tatafo. ta kasance fuskar Telecom consumer na Nigerian Communications Commission (NCC).[165][166]
  • Lancelot Oduwa Imasuen, darekta kuma furodusa a Nollywood. Ya kirkiri makarantan fim na farko a Benin Igbinedion University, Okada, Jihar Edo.
  • Hon. Joe Edionwele, dan siyasa kuma dan majalisa a majalisa ta 8 da ta 9 National Assembly, Nigeria mai wakiltar mazabar Edo ta Tsakiya.
  • Lucky Igbinedion dan siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Edo.[167]
  • Oserheimen Osunbor, Lauya kuma gwamna na wani dan lokaci a jihar.[168]
  • Osagie Ehanire Likitan Najeriya kuma dan siyasa[169][170]
  • Skales mawakin rap na Najeriya, kuma marubci.
  • Nancy Isime Jaruma a Najeriya, 'yar talla kuma sannan a midiya.
  • Adesua Etomi Jaruma a Najeriya
  • BB02 Mawaki
  • Prof. Eghosa Emmanuel Osaghae, farfesa akan harkokin siyasa a Jami'ar Ibadan, Jihar Oyo, Najeriya. ya rike matsayin Vice Chancellor a Igbinedion University, Okada tsakanin 2004-2018. A shekarar 2019, ya kasance shugaban Claude Ake a Jam'iar Uppsala da ke Sweden. A shekara ta 2017, Professor Osaghae ya koyar da siyasa da zamantakewa a Van Zyl Slabbert, Jam'iar Cape Town South Africa. A yanzu yana bin sahun MacArthur. Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi matsayin Director General na Nigerian Institute of International Affairs (NIIA).


Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads