Geoffrey Onyeama
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Geoffrey Jideofor Kwusike Onyeama (An haife shi ne a 2 ga watan Fabrairun shekarar ta 1956) ya kasance shi ne Ministan Harkokin Wajen Najeriya. Onyeama an nada shi Ministan Harkokin Wajen Najeriya ne a watan Nuwamba na shekarar ta 2015, Akarka shin Shugaba Muhammadu Buhari . [1]

Remove ads
Rayuwar farko da ilimi
Onyeama ya kasan ce ya fito daga dangin masanin shari'ar Najeriya Charles Onyeama.[2] Yayi digirinsa na farko, ya kuma Rike (BA) a Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Columbia, New York a shekarar ta 1977, ya kuma gama digirinsa na farko a bangaran Arts (BA), ya karanci Lauya a Kwalejin St John's College, Cambridge A shekara ta 1980. Yana da Digiri na biyu (LL. M) daga Makarantar Tattalin Arziki da Kimiyyar Siyasa ta London a shekarar ta 1982 , da kuma zama kwararre a bangaren Arts (MA) , da Shari'a daga St John's College, Cambridge a shekara ta 1984.[3] Onyeama an shigar da shi a matsayin Lauya na Kotun Koli ta Nijeriya a cikin shekarar ta1983 kuma an kira shi zuwa ga Ingilishi Bar na Grey's a shekarar ta 1981.[4]
Remove ads
Ayyuka

Onyeama ya fara aikin sa ne a matsayin Jami'in Bincike a Hukumar sake fasalin Dokokin Najeriya a Legas daga shekarar ta 1983 zuwa shekarar ta 1984. Sannan ya yi aiki a matsayin lauya tare da .Mogboh and Associate a Enugu, Nijeriya daga shekara ta 1984 zuwa ta 1985, A shekarar ta 1985, ya shiga Kungiyar World Intellectual Property Organization wato (WIPO) a matsayin Mataimakin Jami'in Shirye-shiryen ci gaban hadin gwiwa da alakar waje, Ofishin Afirka da Yammacin Asiya. Ya sami matsayi a WIPO ya zama Mataimakin Darakta Janar na sashen bunkasa a shekarar ta 2009. A watan Nuwamba na shekarar ta 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Ministan Harkokin Wajen Najeriya.[5]
Remove ads
Rayuwar mutum
Onyeama ya yi aure; kuma yana da yara uku. da Matarsa ta yanzu ita ce Sulola; wanda Onyeama ke da yara biyu. da ita, Onyeama ya auri ɗiyar Christian Onoh : Nuzo Onoh kuma suna da ɗa na farko da matar. Onyeama mai suna Candice Onyeama; mai rubutun allo da shirya fim.[6][7][8]

A ranar 19 ga watan Yulin na shekara ta 2020, Onyeama ya shiga keɓewar likita bayan ya sanar da cewa ya samu tabbataccin COVID-19.[9] A ƙarshen watan Agusta na shekara ta 2020, Onyeama ya warke daga cutar COVID-19 na coronavirus; kuma ya koma aikinsa na jagoranci a matsayin HMFA: Mai girma Ministan Harkokin Waje a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya.[10][11][12]
Duba kuma
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads