Nana Gichuru
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Ephex Kanana Gichuru (14 Disamba 1986[1][2] – 22 Satumba 2015) ta kasance 'yar wasan kwaikwayo ta ƙasar Kenya da kuma gidan talabijin. An fi saninta da sunan Nana Gichuru.[3] A matsayinta na 'yar fim an san ta da rawar da tayi a cikin shirin talabijin na Noose of Golde, Demigods da How to Find a husband.[4] A matsayinta na mai shiryawa, itace zata gabatar da shirin Interior Designs, jerin labaran gaskiya na Kenya, kafin mutuwarta. Ta kasance ma'aikaciyar jirgin sama na Kenya Airways. Tayi aure da Richard Wainaina gabanin mutuwarta.
Remove ads
Ayyuka
Gichuru ta yi fice a shirye-shirye da yawa kamar Noose of Gold na shekara ta 2010 da Demigods a shekarar 2011. Sabbin fina-finanta sun kasance a wani wasan barkwanci How to Find a Husband da kuma shiri na kai tsaye wato Interior Designs.
Mutuwa
Da misalin karfe 10 na safiyar ranar 22 ga watan Satumbar 2015, Nana na tafiya a motarta kirar BMW a kan hanyar gabashin Bypass, Utawala, yayinda motarta ta yi karo da babbar motar. Ta mutu a take a wajen. Ta mutu tana da shekaru 28.[5] Mutuwar ta ta zo ne kwanaki goma bayan da ta yi hasashen mutuwar nata a shafinta na sada zumunta.[6][7] An gudanar da bikin tunawa da ita a ranar 30 Satumba 2015 a Cocin Ruaraka Methodist.[8] An binne ta a ranar 2 ga Oktoba 2015 a garin, Kaaga a Meru.
Remove ads
Fina-finai
Hanyoyin Haɗin waje
- Adireshi na musamman http://nanagichuru.com/ Archived 2016-03-13 at the Wayback Machine
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads