Navi Pillay
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Navanethem "Navi" Pillay (an haife ta ranar 23 ga watan Satumba shekara ta 1941) ƙwararriyar masaniyaf shari'a ce ta Afirka ta Kudu wanda ta yi aiki a matsayin Babbar Kwamishinan Kare Haƙƙin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya daga 2008 zuwa 2014.'Yar Afirka ta Kudu 'yar asalin Tamil ta Indiya, ita ce mace ta farko da ba farar fata ba a Kotun Koli ta Afirka ta Kudu,[1] kuma ta yi aiki a matsayin alkaliya ta Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da Shugabar Kotun Hukunta Laifukan Ruwanda. .Wa'adinta na shekaru huɗu a matsayin Babban Kwamishinan a hukumar kare Ƴancin Ɗan Adam ya fara a ranar 1 ga Satumba 2008[2] kuma an ƙara ƙarin shekaru biyu a 2012.[3] Yarima Zeid bin Ra'ad ne ya gaje ta a watan Satumban 2014.A cikin Afrilun shekarar 2015 Pillay ta zama Kwamishina ta 16 na Hukumar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya. Har ila yau, tana ɗaya daga cikin manyan mutane 25 a hukumar yaɗa labarai da dimokuraɗiyya da ƙungiyar masu rajin kare hakkin bil'adama ta Reporters Without Borders ta kaddamar.[4]



Remove ads
Fage
An haifi Pillay a shekara ta 1941 a wata matalauta unguwar Durban, lardin Natal, Tarayyar Afirka ta Kudu.[1] Ita 'yar asalin Tamil ta Indiya ce kuma mahaifinta direban bas ne.[1] Ta auri Gaby Pillay, lauya, a cikin Janairu 1965.[5] Tana da 'ya'ya mata biyu.

Al'ummar Indiya sun tallafa mata da gudummawa,[6][7] ta kammala karatu daga Jami'ar Natal tare da BA a shekarar 1963 da LLB a 1965. Daga baya ta halarci Makarantar Shari'a ta Harvard, ta sami LLM a 1982 da kuma Dikita na Digiri na Kimiyyar Shari'a a 1988. Pillay ita ce 'yar Afirka ta Kudu ta farko da ta sami digiri na uku a fannin shari'a daga Makarantar Shari'a ta Harvard.[8]
Remove ads
Kyaututtuka
A cikin shekarar 2003, Pillay ta sami lambar yabo ta Gruber don 'Yancin Mata.
An ba ta digirin girmamawa
- Jami'ar Fasaha ta Durban - Jami'ar da ke garinsu na Durban, Afirka ta Kudu,
- Jami'ar Durham,
- Makarantar Shari'a ta Jami'ar City ta New York,
- Makarantar Tattalin Arziki ta London, Jami'ar Rhodes,
- Jami'ar Leuven
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads