Sameera Reddy
Jarumar wasan kwaykwayo a india From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Sameera Reddy (an haifi Sameera Raddy a ranar 14 ga watan Disamba, shekarar alif 1980), tsohuwar 'yar wasan Fim ce ta Indiya wadda ta fara yin fina-finai a finafinan Hindi. Ta kuma fito a cikin 'yan fina-finan Harsunan Telugu, Tamil da Malayalam.

Sameera Reddy ta fito a karon farko a fim ɗin 2002 Maine Dil Tujhko Diya. An fi saninta da tauraruwar fina-finai kamar su Darna Mana Hai (2003), Musafir (2004), Jai Chiranjeeva (2005), Taxi Number 9211 (2006), Ashok (2006), Race (2008), Varanam Aayiram (2008), De Dana Dan (2009), Aakrosh (2010), Vettai (2012) da Tezz (2012).
Remove ads
Farkon rayuwa
An haifi Sameera Raddy a ranar 14 ga watan Disamba shekarar 1980 a Mumbai, Maharashtra ga mahaifin Telugu da mahaifiyar ta yar Kannadiga.[1][2] Mahaifiyarta Nakshatra,,[3] wadda ake kira da Niki daga 'ya'yanta da kafofin watsa labarai, kwararriyar masaniya ce a kan kananan halittu "microbiologist" kuma ta yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu.[4][5] Tana da 'yan'uwa biyu, Meghna Reddy, tsohuwar VJ da supermodel,[6] da Sushama Reddy ,' yar wasan kwaikwayo na Bollywood kuma abin kwaikwayo,[7] duka ya yi ne a gare ta.[8] Ta yi karatun ta a Bombay Scottish School a Mahim, Mumbai kuma ta yi karatun digiri a Sydenham College .
Sameera Raddy ta bayyana kanta a matsayin " tomboy " da "mummunar haihuwar cikin dangi", an Ambato ta da cewa: "ina da kiba, ina da tabarau kuma kayan jin dadi na bai ragu sosai ba, har zuwa shekaru 19."[8]
Remove ads
Aiki

Sameera Reddy ta fara bayyana a cikin ghazal mawakiyar Pankaj Udhas's "Aur Aahista" a bidiyon wakar a 1997.[9] Sameera Raddy an shirya za ta fara fitowa a matsayin yar wasan kwaikwayo a finafinan Tamil na Saravana Subbiah Citizen, a farkon 2000s, amma daga baya hakan bai kasance ba.[10] Ta ɗauki hankalin Bollywood kuma an sa ta cikin muhimmiyar rawa a fim ɗin Hindi a shekarar 2002 Maine Dil Tujhko Diya. A shekarar 2004, ta bayyana a Musafir, gaban Anil Kapoor, Aditya Pancholi da Koena Mitra .

Sameera Raddy ita ce kuma 'yar wasan fim ɗin Indiya ta farko da ta sami wasan bidiyo na kanta, Sameera the Street Fighter. Wannan bidyon wayar hannu mutane sama da miliyoyi ne suka saukar da shi da miliyoyin magoya baya kuma yana samuwa ga masu amfani da wayar hannu a duk Indiya.
Remove ads
Rayuwarta
Sameera Reddy babbar masoyiyar Oprah Winfrey ce . Ta sadu da Oprah a yayin ziyarar da ta kawo a Indiya a wurin tarbar maraba da Parmeshwar Godrej ya shirya. Kamar yadda yadda aka bayar da rahoto a talabijin ɗin "Celebrit" cewa burge Sameera Raddy ta Saree, ta gabatar mata wani irin Saree a matsayin kyauta tata na actress kafin ta bar India.[11]

Sameera Reddy ta auri Akshai Varde, ɗan kasuwa a ranar 21 ga watan Janairu 2014. Bikin aure ne na gargajiya.[12][13] Suna da ɗa wanda aka haifa a cikin 2015. [14] Ma’auratan sun haifi diya mace a ranar 12 ga Yuli 2019.[15]
Wasu ayyukan
Sameera Reddy ta kasance alkali ya a gasar Sri Lanka ta Duniya a 2012.[16]
Fina-finai
Remove ads
Bidiyon waka
Bidiyon wasanni
Kyaututtuka da kuma gabatarwa
Duba kuma
- Jerin fina-finan Hindi
Manazarta
Hanyoyin hadin waje
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads