Siyasa

From Wikipedia, the free encyclopedia

Siyasa
Remove ads

Siyasa hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a hade, ko a tare, ko a kungiyance cikin manufa daya[1][2]. Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da mabam-bantan ra'ayoyi, kabilu da addinai, a birane da kasashe[3][4]. A manyan kashashe mutane da dama kan ɗauki dogon lokaci wajen tsayar da yarjejeniyar siyasa. Wadannan mutane kuma su ake ƙira da Yan'siyasa[5]. Yan-siyasa da kuma wadansu mutane kan hadu domin samar da Gwamnati da tafiyar a tare. Karatun tafiyar da gwamnati a jami'a ana kiranshi da Ilimin kimiyar siyasa da (turanci Political Science, ko Political Studies).

Quick facts Bayanai, Ƙaramin ɓangare na ...

Siyasa al'amari ne da yake kunshe da manufofi da kuma tsare-tsare.

Fayil:Manyan Jamiyyun siyasa biyu a Najeriya.jpg
Apc da pdp manyan Jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya

A ma'anar ko yaushe Siyasa na nufin hanyar da kasashe ke bi domin aiwatar da mulki ko gwamnati, da kuma hanyar da gwamnatoci ke bi wajen aiwatar da dokoki. Ana kuma yin siyasa a wasu guraren kamar Kamfanoni, kungiyoyi, makarantu, masallatai da majami'u.

Remove ads

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads