Tagwaye

From Wikipedia, the free encyclopedia

Tagwaye
Remove ads

Tagwaye ko Yan biyu na nufin waɗanda akayi rainon cikin su tare kuma aka haife su a tare. Ana samun tagwaye ne daga cikin halittu masu mama kuma masu haihuwa.

Thumb
Tagwaye Mark Kelly da Scott Kelly, ya sama jannatin kasar Amurika.
Quick facts Bayanai, Ƙaramin ɓangare na ...
Thumb
Tagwaye ko yan biyu

[1][2][3] Yawancin tagwaye sunyi kama da junan su a ta fuska ko ɗabi'a koma duka biyun, sai dai akan samu waɗanda basuyi wata kama ba, amma wannan ba kasafai ba.[4]

Remove ads

Ɗan Adam

Ana samun tagwaye sosai a haife haifen da akeyi na Adam. A kasar Amurika an samu tagwaye daga kaso tara da ɗigo tara 9.4 zuwa 16.7 (18.8 zuwa 33.3 na tagwaye) daga cikin haihuwa 1000 da akeyi tsakanin shekarun alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin 1980 da shekarar alif dubu biyu da tara 2009.[5] Kabilar Yarbawa sune ke kan gaba wajen haihuwar tagwaye a duniya. Inda ake samun casain 90 zuwa ɗari 100 cikin haihuwa dubu ɗaya 1000,[6][7][8] an haƙiƙance hakan na samuwa ne sakamakon cin Doya da ta zama babban abincin Yarbawa wanda ana samun sinadarai na samun tagwaye a cikin Doya.[9][10] In Central Africa, akwai goma sha takwas zuwa talatin 18–30 twin sets (or 36–60 twins) per 1,000 live births.[11] a yankin nahiyar Amurika, Indiya, Bangladesh, Nepal da Kudu maso gabashin Asiya, nan ne ake samun mafi ƙaranci na haihuwar tagwaye inda kawai kaso shida 6 zuwa tara 9 ake samu cikin haihuwa dubu ɗaya 1000. Arewacin Amurika da Turai kuwa ana samun tagwaye ne cikin kaso tara 9 zuwa goma sha shida 16 na haihuwa dubu ɗaya 1000.[11]

Mata waɗanda a dangin su ana samun tagwaye suma sukan haifi tagwaye, kenan haihuwar tagwaye kan zamo gado amma ba kasafai ba.[12][13] Wasu dalilan da kan sanya haihuwar tagwaye sun haɗa da yanayin abinci da aiyukan Kimiyya.[14] Hakanan kuma wasu matan kan sha wasu magunguna da niyya domin haihuwar tagwaye.[15]

Remove ads

Dabbobi

Ana samun haihuwar tagwaye a Dabbobi kamar Maguna, Tumaki, Karnuka, Shanu, Akuya da dai sauran su.

Thumb
wasu tagwayen Shanu.

Hotuna

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads