Timbuktu

From Wikipedia, the free encyclopedia

Timbuktu
Remove ads

Timbuktu birni ne, da ke a yankin Tombouctou, aƙasarnMali yammacin Afirka. Jami'ar Sankore da sauran makarantun addinin musulunci ko madrasas suna cikin gari. Garin yana da mahimmanci ga tunani da kuma addini a ƙarni na goma sha’biyar 15 da goma sha’shidda 16. Yana da mahimmanci wajen yada addinin Musulunci ta hanyar Afirka a wancan lokacin. Akwai manyan masallatai guda uku: Djingareyber, Sankore da Sidi Yahya.Tunatarwa ne game da zamanin zinar Timbuktu. Kullum ana gyara su, amma ana musu barazana saboda hamada tana yaduwa. [1]

Quick Facts Wuri, Babban birnin ...
Thumb
Masallacin Djingareiber, Timbuktu
Thumb
Massallaci, Sankore Timbuktu
Thumb
Masallacin timbuktu
Thumb
taswirar timbuktu

Mutanen Songhay, Abzinawa, Fulani, da na Mandé sune ke zaune a Timbuktu. Shi yana kilomita goma sha’biyar 15 arewa daa Kogin Neja . Akwai hanya ta hamadar Sahara daga gabas zuwa yamma kuma ana amfani da wannan don kasuwanci . Akwai wani daga arewa zuwa kudu . Waɗannan hanyoyi biyu sun haɗu a Timbuktu. Yana da wani entrepôt ga dutse gishiri daga Taoudenni . Wannan yana nufin cewa an kawo gishirin nan kuma a sayar wa wasu mutane su kai shi wani wuri, amma ba a biyan haraji .

Wurin ya taimaka mutane daban-daban sun haɗu, don haka mutanen gida, Abzinawa da Larabawa suka haɗu anan. Tana da dogon tarihi na cakuɗa kasuwancin Afirka, don haka ya zama sananne a Turai saboda wannan dalili. Saboda haka, mutanen yamma suna yawan tunanin Timbuktu a matsayin na musamman. Tana da yanayin hamada mai zafi ( BWh a cikin ƙirar yanayin Koeppen ).

Timbuktu ya ba Musulunci na duniya damar bincike da nazari. [2] An rubuta littattafai masu mahimmanci kuma an kwafa su a Timbuktu a cikin ƙarni na 14. Wannan ya sa garin ya zama cibiyar rubutu a Afirka.

Remove ads

Hotuna

Manazarta

Loading related searches...

Wikiwand - on

Seamless Wikipedia browsing. On steroids.

Remove ads