Mali
From Wikipedia, the free encyclopedia
Remove ads
Mali da Turanci (Mali): Da Faransanci (Meli) ƙasa. ce da ke a yammacin Afrika. Mali tana cikin manyan ƙasashen Afrika guda 8, ta na da faɗin ƙasa kimanin murabba'i (1,240,000,Km) (480,000 sq, mi), kuma tana da yawan jama`a kimanin miliyan (19).1. Bincike ya nuna cewa (67)% na mutanen ƙasar shekarunsu bai wuce ashirin da biyar (25) ba, bisa ƙidayar da aka yi a shekarar (2017).Bamako shi ne babban birnin ƙasar Mali.










Remove ads
Tarihi:

Waɗannan ƙabilu Soninke da Mandinka ko (Mandingo da Malinke) sun ɓalle daga ƙasar Kongo a shekarar (1230) daga nan sarkin madingo Sundiata Keita sai ya yi ƙungiya ta waɗannan ƙabilu guda uku a gefan tafkin chadi, sannan masarautar Mali aka ƙirƙirota a wannan lokacin tafi masarautar Ghana. Mansa Musa yana da baban magame a ƙasa bayan sarki Sundiata Keita shi ne ɗan afirka na farko da ya je aikin Hajji da ƙafa a shekar (1324) ta hanyar misra, a wannan shekarar kuma aka zamar da Tomboucou kasuwar sayar da zinari da koyar da Addinin Musulunci.
A ƙarshen karni na (14) Abizinawa suka zo daga kudancin hamada suka mamaye wannan birni a shekarar (1500)sai suka tsawaita ikonsu zuwa sama da tafkin issa.



A ranar (22) ga watan satumban, shekarar (1960) sai Jamhuriyar Sudan da Senegal suka samu 'yancin kai daga Faransa, suka haɗe tare suka zama tarayyar Mali bayan watanni sai Senegal ta ɓalle daga Jamhuriyar sudan. daga nan sai aka samata sunan Jamhuriyar Sudan. A shekarar (1991), aka yi gwamnati ta wucin-gadi daga nan aka kawo ƙarshen hukunci mai tsanani, kuma a shekarar (1992) aka yi zaɓe na farko a sabuwar dimokwaraɗiyya, shugaba Alfa Umar Kunare ya lashe zaɓen a shekarar (1997) sai aka sake zaɓensa a Karo na biyu kuma a shekara ta (2002) aka yi wani zaben, sai Ahamadu Tumane Ture ya lashe zaɓen har ila yau.[1]

Remove ads
Hotuna:






- Begnimatou, Mali
- Tutar kasar
- Coat of Arms
- Wani ɗan talla a Kasar Mali.
- Tsohon Masallaci a Ƙasar Mali.
- Ginin ƙauye a Mali.
- Wani mutum ɗan ƙasar Mali.
- Mawaƙan gargajiya a ƙasar Mali.
- Mawaƙa a Ƙasar Mali.
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Remove ads